Hadarin Motoci 4 A Dungal: Mutane 10 Sun Rasu, 10 Sun Ji Rauni

0
927

Umar Saye, Daga Bauci

WANI mummunan haɗarin mota da ya auku a ƙauyen Dungal da ke kan hanyar Jos zuwa Bauci ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 9 yayin da kuma mutane 11 suka samu munanan raunuka inda suke kwance a asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Bauci.

Kwamandan rundunar kiyaye haɗurra ta ƙasa na Jahar Bauci, Mista H. S. Olatunji ya ce, haɗarin ya auku ne sakamakon wuce juna ba bisa ƙa’ida ba da kuma tuƙin ganganci haɗe da gudun da ya wuce ƙima da misalin ƙarfe shida da minti 35 na yammacin ranar Litinin inda motoci uku suka haɗu, ciki akwai farar bas mai lamba DE 219 FST da wata mota ƙirar fijo mai lamba BC 428 GWA mai launin ruwan toka sai kuma wata ƙirar fasat mai lamba PPL abin da aka iya ganewa daga cikin alƙaluman lambobinta.

Mutane shida sun ƙone a cikin bas yayin da kuma mutane 4 suka mutu a cikin fijon yadda jimla ta bayar da mutane goma yayin da mutane 11 kuma suke kwance a asibiti.

Don haka Mista Olatunji ya gargaɗi direbobi su kasance masu natsuwa da tuƙi tare da haƙuri don kiyaye rayuwa da dukiyar al’umma. Ya ce wasu daga cikin mutanen da suka rasu ba za a gane su ba, kuma haɗarin ya haɗa da mutane 20.

Wani wanda lamarin ya faru kan idonsa ya bayyana wa wakilinmu cewa, direba guda ne yana gudu ya zo wuce wata tankar mai wacce ba ta ɗauke da kaya a lokacin da mota ƙirar fijo take tahowa sai aka yi taho mu gama biyu daga cikin motocin suka kama da wuta. Amma tankar ba wanda ya rasu a ciki, sai ko bayan zuwan jami’an hukumar kwana-kwana da suka kashe wutar motocin biyun ya ga an zaro gawarwaki 4 a cikin fijon yayin da aka zaro bakwai daga motar bas aka nufi asibiti da su tare da waɗanda suka ji raunuka a motar jami’an hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.