Jonathan Ya Yi Wa Majalisarsa Garambawul

0
520

SHUGABAN    ƙasa Dokta   Goodluck Jonathan, ya yi ƙaramin garambawul, inda ya koma da minista a ma’aikatar wutar lantarki, Mista Darius Ishaku zuwa ma’aikatar harkokin Neja Delta a yayin da minista a ma’aikatar harkokin Neja Delta, Hajiya Zainab Ibrahim Kuchi, ta maye gurbin Mista Ishaku a ma’aikatar wutar lantarki.

Mista Darius Ishaku ne muƙaddashin ministan wutar lantarki tun da Furofesa Barth Nnaji ya sauka daga muƙamin ministan wutar lantarki a ‘yan watannin baya.

Mai bai wa shugaban ƙasa a kan kafafen yaɗa labarai da yayatawa, Dokta Reuben Abati, ya ce shugaban ƙasa ne ya bayar da sanarwar yin ƙaramin garambawul a taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta gudanar a jiya, Laraba, a Abuja. Ya ce ministocin biyu za su fara aiki a sababbin ma’aikatunsu a makon gobe.

Kamar yadda ya ce, Shugaba Jonathan ya bayar da umarnin cewa, majalisar ba za ta amshi sababbin takardu a kan kwangiloli bayan ranar 30 ga Nuwamba ba, kuma wannan na nufin lallai ne a bayar da takardun kwangiloli a ƙarƙashin kasafin kuɗin 2012 ya zuwa wannan rana.

FEC ta amince da kwangiloli na kusan Naira biliyan 11.7 don gina rukunin farko na babban asibiti a gundumar Gwarimpa mai gadaje 220 da ginin cibiyar hukumar ɗa’ar ma’aikata mai hawa 13.

Minista a ma’aikatar yankin Abuja, Misis Oloye Olajumoke Akinjide, ta yi bayanin rukunin aikin asibitin na biyu ya ƙunshi sanya wa asibitin kayayyaki bayan kammala aikin rukunin farko.

Haka kuma ministan ayyuka, Mista Mike Onolememen, ya yi bayanin cewa, FEC ta amince da shirin kula da gyara manyan hanyoyi a cikin ƙasar nan da ma’aikatar ayyuka za ta gudanar ba tare da ɓata lokaci ba.

Mista Mike Onolememen ya yi bayanin cewa, tuni ma’aikatar tana yin aiki a kan hanyoyi da gadojin da ruwa ya lalata su a cikin ƙasa a sanadiyyar ambaliyar ruwan da aka samu a bana.

Haka kuma a yayin jawabi, Dokta Abati ya musanta wutar lantarki da ake samarwa ta ragu a yayin amsa wata tambaya. Ya ce ‘yan Najeriya ma suna yaba wa gwamnati game da samar da ƙaruwar wutar lantarki a ƙasa.

Mai ba shugaban ƙasa shawara ɗin ya ce in har shugaban ƙasa ya ɗauki wani mataki game da wutar lantarki, to, a tabbatar da cewa, ƙoƙari ne na inganta sashin wutar lantarki ɗin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.