An Bada Kwangilar Gyara Madatsar Ruwan Kankia

0
643

Abdullahi Mohammed, Daga Katsina

Al’ummomin ƙaramar hukumar Kankia za su ɗara a yayin da gwamnatin tarayya ta bada kwangilar gyara madatsar ruwan Kankia.

Aikin kwangilar da zai ci Naira miliyan ɗari da arba’in kuma za a kammala aikin a cikin watanni uku.

Ɗan majalisar wakillai da je wakiltar mazaɓar Kankia da Kusada da Ingawa, Alhai Ahmed Babba Kaita, ne ya faɗi haka a lokacin da yake zagawa da manema labarai wajen aikin dam.

Ya ce shekaru goma sha biyu ke nan da aka fara aikin dam ɗin amma aka yi watsi da shi sai yanzu a lokacin wakilcinsa ya matsa aka sanya aikin cikin kasafin kuɗi na dubu biyu da sha ɗaya.

Ya ce da zaran an kammala aikin gyara dam ɗin, bayan samar da da ruwan sha, za a riƙa noma rani a wurin.

Alhaji Baubba Kaita ya bayyana cewa, kashi na biyu na aikin da zai ci kuɗi Naira ɗari biyu da sha uku an rigaya amsa kuɗin a cikin kasafin kuɗi na wannan shekara.

Sai ya hari ya kwangilar da su bi ƙa’idar aikin kwangilar da aka yi yarjejeniya da su.

Ɗan kwangilar, Alhaji Bello Bakori na kamfanin Ben Ladan ya yi alƙawarin yin aikin mai inganci tare da yi a kan lokaci.

Shi dai wannan aikin dam na Kankia yana ɗaya daga cikin aikacen-aikace da gwamnatin tarayya take badawa na mazaɓu ‘yan majalisar wakilai da  na dattijai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.