Gwamnatin Kano Ta Banƙado Gurbin ’Yan Kano Samar Da 1,500

0
1104

DAGA SANI AHMED SAGAGI

A MAKON da ya gabata ne shugaban hukumar bayar da shawara da jagoranci ta Jahar Kano, Alhaji Habu Ibrahim Cagge ya bayyana wa manema labarai cewa, a yanzu haka ya sami nasarar banƙado gurabe kimanin dubu ɗaya da ɗari biyar a dukkannin faɗin ƙasar nan wanda kaso ne na ‘yan asalin Jahar Kano a hukumomin ɗaukan ‘yan sanda da sojoji sai kuma hukummomin jami’an kula da shige da fice ta ƙasa da kuma hana fasa ƙwauri, sauran kuma sun haɗar da hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa.

Habu Ibrahim fagge ya ƙara da cewa, a Gwamnatin baya ba ta kula da irin wannan gurabe da ake warewa don ‘yan Kano, amma yanzu tuni sun tura ‘yan Kano sun cike waɗannan kujeru a cikin tsawan watanni goma sha biyar da ya yi a ofis a saboda haka ya ja hankalin shugabannin ƙananan hukumomin mulkin Jahar Kano su riƙa leƙawa don ƙarfafa wa ‘yan asalin ƙananan hukumomin nasu gwiwa a kodayaushe musammam waɗanda suke makarantar kula da harkokin man fetur da ke Warri sai kuma waɗanda ke cibiyar horar da sojoji da ke Zariya Minna da Kaduna.

Alhaji Ibrahim Fagge ya kuma tabbatar da cewa, an kafa hukumar ne a shakara ta 2000 da suke gabata a lokacin wa’adin mulkin Gwamna Kwankwaso na farko, kuma haƙƙinta ne jagoranci da bayar da shawara ga ‘yan a salin Jahar Kano musamman a fuskar kasuwanci da ayyukan gwamnatocin jaha da tarayya don samun ingantuwar rayuwar al’umma jahar.

Haka kuma ya bayyana cewa, sun samu nasarar wayar da kan ‘yan asalin Jahar Kano kan su koyi tafiya jahohin kudu kamar yadda su ma suke zuwa nan arewa suna zama tare da neman arziƙinsu a nan, wanda ma ya ce ‘yan asalin Kano sun fara koyon zaman Kudu.

Da ya koma ta kan Gwamnan Jahar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso gode masa ya yi game da kuma dukkan waɗanda suka samu shiga cikin shirin kan su zamo jakadu nagari don su zama abin misali ga al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.