Cutar Sida Ta Ragu A Jahar Adamawa

0
582

MUHAMMAD SHAFI’U SALEH, Daga Yola

An bayyana cutar Sida (HIV/ADIS) da cewa, ta ragu nesa ba kusa ba a Jahar Adamawa.

Shugabar Ƙungiyar yaƘi da yaɗuwar cutar (ADSCA) a jahar, Dokta Halima Nyako ta bayyana haka da take gabatar da jawabinta a yayin bikin ranar masu ɗauke da cutar ta duniya da aka yi a dandalin wasa na Mahmoud Ribaɗu da ke Yola.

Dokta Halima Murtala H. Nyako ta ci gaba da bayyana cewa, a halin da ake ciki gwamnatin jahar ta buɗe asibitoci a ɗaukacin yankunan jahar don kyautata yanayi da kuma samun kula ta musamman ga mutanen da suke ɗauke da cutar ta ce bisa wannan ƘoƘari ne a yanzu jahar ta zama ta biyu daga cikin jerin jahohin yankin arewa maso gabas a adadin mutanen da suke ɗauke da cutar Sida ɗin.

Ta ci gaba da bayyana cewa, gwamnatin jahar ta ware kimanin Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari huɗu wajen kula da hukumomin kula da gwaje-gwajen cutar, ta ce gwamnatin tana kashe wasu Ƙarin Naira dubu arba’in da biyar ga kowane mutum ɗaya mai ɗauke da cutar duk shekara, kana gwamnati tana kashe Naira dubu ɗari biyu da hamsin wajen aikin bada horo ga waɗanda ke kula da masu cutar a Jahar Adamawa.

Dokta Halima Nyako ta kuma yi nuni da cewa, gudunmawar da gwamnatin jahar ke samu daga babban bankin duniya wanda kuma ake ɗaukar ɗawainiyar mutanen da ke ɗauke da cutar zai kawo Ƙarshe a 2015, don haka ta ce gwamnatin jahar za ta tsaya da Ƙafafunta wajen ci gaba da samar da yanayi mai inganci ga masu ɗauke da cutar ta Sida.

Shugabar Ƙungiyar yaƘi da cutar sida ta Jahar Adamawa, Dokta Halima Nyako ta nemi haɗin kan da goyon bayan jama’ar jahar, don haka ne ma ta ce lokaci ya yi da jama’ar jahar za su bada duk goyon bayan da ya kamata wajen ganin an samu nasarar kawar da cutar gaba ɗaya.

Haka shi ma kodinetan yaƘi da cutar Sida a Jahar Adamawa, Suleiman M. T. Buta ya bayyana irin nasarorin da ya ce sun cimma a jahar, inda ya ce sun cimma kyakkyawar nasara a ƘoƘarin da suke na yaƘi da cutar sida a jahar, don kuwa a 2010 jahar ta zo ta biyu na masu ɗauke da cutar a yankin arewa maso gabas, amma a bana sai ga shi jahar ta zo ta biyu daga cikin jahohin da cutar ta ragu ɗayani.

Ya ce kuma sun cimma nasara inda majalisar dokokin jahar ta amince da kafa doka da ta bai wa Ƙungiyar damar samun cin gashin kanta kana gwamnan jahar, Murtala Nyako ya ba su damar samun horo inda yanzu suke da Ƙwararrun ma’aikata, ya ce kuma uwargidan gwamnan, Halima Nyako tana bada duk gudunmawar da ta dace da hakan ya ba su damar cimma nasara cikin Ƙaramin lokaci.

Ya ce a shekarar 2010 jahar tana da mataki 6.8 ne na mutanen da ke ɗauke da cutar sida wanda hakan ke nufin ita ke kan gaba a jahohi 6 na yankin, amma a wannan lokaci tana mataki 3.6 ne, don haka ba Ƙaramar nasara suka samu ba, bisa jagorancin uwargidan gwamnan, Dokta Halima Nyako da kuma haɗin kan sarakunan da ke Jahar Adamawa.

Kodinetan Ƙungiyar ta SCA ta Jahar Adamawa, ya kuma nuna damuwa matuƘa game da yadda Musulmi kamar ba su damu da cutar ba, inda ya ce Musulmi ne kawai ke aure ba tare da gwaji ba, amma kiristoci gwaji a wurinsu dole ne, don haka Fasto ba zai ɗaura aure ba sai an yi gwaji cikin wata uku kafin aure, sai ya yi kira ga Musulmi da su ɗauki maganar gwaji da muhimmanci kafin aure zai taimaka wajen samun kariya daga kamuwa da cutar sida.

Haka shi ma, ɗaya daga cikin likitocin da ke kula da masu ɗauke da cutar, Dokta Longjo Austin Yusuf ya yi Ƙarin bayani cewa, kimanin mutane dubu 122, 945 ne suka yi wa gwaji a shekarar 2008 inda a yanzu kuma suke ɗauke da cutar Sida a Jahar Adamawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.