Gwamna Yakowa Ya Ƙaddamar Da Aikin Hanyar Garu Zuwa Bundun Kasuwa

0
972

Isah Ahmed, Daga Jos

GWAMNAN Jahar Kaduna, Mista Patrick Ibrahim Yakowa ya Ƙaddamar da fara aikin hanyar da ta tashi daga garin Garun Kurama zuwa Bundun Kasuwa da ke Ƙaramar hukumar Lere a Jahar Kaduna.

Da yake jawabi, Gwamna Yakowa ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta sanya harkokin samar da zaman lafiya da haɗin kan al’ummar Jahar Kaduna a gaba. Don haka ya ce gwamnatin ta kafa kwamitin mutane 60, don tattauna matsalolin da suke damun al’ummar jahar tare da ba wa gwamnati shawarwarin hanyoyin da za a Ƙara samun zaman lafiya a jahar.

Ya ce zaman lafiya da haɗin kai su ne ginshiƘin ci gaba domin, su ne za su bayar da damar a kawo abubuwa na ci gaba kamar hanyoyi da makarantu da asibitoci da bunƘasa aikin noma da dai sauransu.

Ya ce duk wanda yake shugabanci yana buƘatar addu’a da shawarwari, don haka ya yi kira ga al’ummar jahar su ci gaba da yi wa gwamnatin jahar addu’o’i  tare da ba ta shawarwari.

Ya miƘa godiyarsa ga dukkan sarakunan Jahar Kaduna, musamman na Ƙaramar hukumar Lere kan goyon bayan da suke bai wa gwamnatin Jahar Kaduna kan ƘoƘarin samar da zaman lafiya a jahar.

Daga nan ya yi kira ga kamfanin da aka bai wa aikin hanyar su tabbatar sun kammala aikin kan lokaci da kuma inganci.

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Lere, Birgediya-Janar Abubakar Garba Muhammad Lere (ritaya), ya bayyana matuƘar farin cikinsa da Ƙaddamar da fara aikin wannan hanya.

Ya tabbatar wa gwamnan cewa, za a ci gaba da zaman lafiya a wannan Ƙaramar hukuma.

Har ila yau, ya tabbatar wa gwamnan cewa, za su ci gaba da ba shi goyon baya kan dukkan ayyukan da ya sanya a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.