Rigakafin SanƘarau: An Nemi ’Yan Jarida Su Wayar Da Kan Jama’a

0
1028

Muhammad Sani  Chinade, Daga Damaturu

An nemi ‘yan jarida da su ci gaba da ayyukansu na wayar da kan jama’a dangane da muhimmancin fitowa domin karɓar allurar rigakafin cututtukan da ke addabar jama’a musamman cutar nan ta sanƘarau da ta sako kai a yanzu.

Wannan kira dai ya fito ne daga bakin shugaban kwamitin wayar da kan jama’a dangane da rigakafin ciwon sanƘarau na Jahar Yobe, Alhaji Muhammad Abubakar Babeh a yayin da ya yi jawabi ga manema labarai a garin Damaturu dangane da rigakafin cutar ta sanƘarau da ake ƘoƘarin farawa a dukkan faɗin Jahar ta Yobe.

Alhaji Muhammad Babeh ya Ƙara jaddada buƘatar da ke akwai na ‘yan jarida da kafofin yaɗa labarai su Ƙara Ƙaimi wajen ƘoƘarin da suke yi a kullum wajen wayar da kan jama’a da su karɓi wannan kira don amincewa a masu rigakafin cutar ta sanƘarau, su da ‘ya‘yan su kasancewar wannan rigakafi hatta masu shekaru 29 ya zuwa Ƙasa duk za a iya masu.

Don haka akwai buƘatar jama’a su bada haɗin kai don samun nasarar kawar da cutar daga cikin jama’a kafin ta yaɗu har ma ta kai ga zama annoba wadda a Ƙarshe lamarin ka iya canza launi ya zama wani abu daban.

Shugaban kwamitin wayar da kan jama’ar ya Ƙara da cewar, wannan aiki na rigakafin cutar ta sanƘarau za a Ƙaddamar da shi ne a wannan wata na Disamba, don haka samun nasarar sa ya ta’allaƘa ne da irin taimakon wayar da kan jama’a da za a iya samu daga ‘yan jaridu da kuma kafofin yaɗa labarai ganin cewar, su ne Ƙashin bayan kowane irin ci gaba da za a iya samu a tsakanin al’umma.

Tun farko da ya ke jawabi ga manema labarai dangane da wannan aiki na rigakafi, darakta-janar na hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko (PHC) na Jahar Yobe, Alhaji Lawan Kawu Ibrahim wanda daraktar hukumar ta PHC, Dokta Hauwa Larai Goni Fika ta wakilta ya bada tabbacin bada goyon baya don ganin an kai ga nasarar wannan muhimmin aiki na rigakafi.

Ya Ƙara da cewar, wannan rigakafi ba shi da illa, za kuma a samar da kati na musamman ga dukkan wanda aka masa da a Ƙarshe ake buƘatar da a adana shi don gaba.

Wannan aiki na rigakafi za kuma a gudanar da shi a cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban da ke jahar da kuma wasu asibitoci ta yadda dukkan waɗanda suka cancanta a yi masu zai matuƘa ya halarci wurin da ake gudanar da aikin na rigakafi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.