Shirin MNCHW Zai Shayar Da Yara Miliyan 1 Sinadaran Ƙara Kuzari

0
848

Umar Saye, Daga Bauci

AƘALLA yara miliyan ɗaya ne za su ci moriyar shayar da sinadaran Ƙara lafiya na ‘Bitamin A’ da wasu sinadaran kariya ga Ƙananan yara ‘yan Ƙasa da shekaru biyar a Jahar Bauci (MNCHW).

Babban sakatare a hukumar lura da lafiya a matakin farko ta Jahar Bauci, Dokta Nisser Aliyu Umar, ne ya bayyana haka cikin jawabinsa a wajen Ƙaddamar da shirin inganta lafiyar Ƙananan yara ‘yan Ƙasa da shekaru biyar da aka Ƙaddamar a asibitin Unguwar Kur da ke Bauci.

Dokta Nisser ya bayyana cewa, za a share mako guda ana zagawa don bayar da sinadaran inganta lafiyar Ƙananan yara da kuma magungunan tsutsar ciki da kiyaye yaran daga kamuwa da cututtuka. Don haka ya shawarci iyayensu fito da yaransu don amsar allurar da magungunan waɗanda ake bayar da su kyauta.

Malam Sabo Burai shi ne shugaban shirin bayar da sinadarai ga Ƙananan yara na Jahar Bauci, cikin hirarsa da manema labarai bayan Ƙaddamar da shirin ya bayyana cewa, za a gudanar da shirin ta hanyar bayar da sinadaran a cibiyoyin kiwon lafiyar da aka ware, don haka ya ce za a ba kimanin yara miliyan guda a duk faɗin Jahar ta Bauci.

Ita ma shugabar asibitin mata da yara na unguwar Kur, Hajiya Hafsat Abdullahi Bello a nata jawabin ta ce za su tabbatar da cewa, sun yi adalci wajen ganin kowane yaro ya ci moriyar shirin, haka kuma irin kayan da ake rabawa na tsafta kamar sabulai da omo da sauran magungunan da aka samar, kowane yaro ya zo wannan cibiya tasu zai samu nasa rabon kamar yadda aka tanada masa a hukumance.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.