Yadda Za A Magance Al’amuran Tsaro A Najeriya

0
1856

HaƘƘin kowace gwamnati ne ta kare tsaron rayuka da lafiya da kuma dukiyar al’ummarta. Gwamnati ita ce ke da alhakin kulawa da dukkan al’amuran mutanen da ke ƘarƘashinta, baƘi, ne ko ‘yan Ƙasa, kula da dukkan dangogin tsaro yana kan hukuma tuna daga tsaron kan iyaka, kula da shige da fice ta sama da ta ruwa. Tun da dukkan masu kayan sarki ko aikin ɗamara suna ƘarƘashin hukuma ne kuma da dukiyar al’ummar Ƙasa ake biyansu albashi. Kamar kuma yadda muka sani shugaban Ƙasa shi ne shugaban kwanmandan askarawan Ƙasar nan baki ɗaya, dukkan wani abu da yake da alaƘa da tsaro shugaban Ƙasa shi ne mutum na farko a kan wannan al’amari.

Sanin kowane ɗan Najeriya ne cewa, sha’anin tsaro ya taɓarɓare a wannan lokaci da ake fuskantar matsin rayuwa. al’amura na Ƙara dagulewa a yayin da aikin yi ya yi Ƙaranci, jami’o’i da kwalejoji kuma suna ta Ƙara ƘyanƘyasar sababbin masu kammala karatu, haka kuma jama’a na ta Ƙara aure da haihuwa, al’umma na Ƙaruwa, ita kuma gwamnati na ta Ƙara faɗaɗa tunani wajen Ƙarin samun hanyar kuɗin shiga. A daidai wannan lokaci ne kuma al’ummar Ƙasa suka shiga cikin wani hali na zullumi da fargabar abubuwan da ka iya zuwa su zo waɗanda suka shafi sha’anin tsaron rayuka da dukiyoyi.

Sanin kowa ne, a ‘yan shekarun da ba su wuce 15 ba an sami hasarar rayuka da dukiyoyi masu ɗimbin yawa, ko dai ta hanyar fashi da makami ko rikicin Ƙabilanci ko rikicin addini ko sanadiyyar tashin bam ko haɗura a kan manya da Ƙananan hanyoyinmu, kuma ta wasu hanyoyin da ba waɗannan ba wanda Allah ne kaɗai ya san adadinsu a wannan Ƙasa tamu mai al’umma kusan miliyan 167 da kuma Ƙabilu daban-daban, baya ga tashe-tashen hankula da rigingimun Ƙabilanci da na addini da suka sha faruwa kuma suke faruwa a daidai lokacin da Ƙasar ta samu ɗimbin dukiyar da ba a taɓa samu ba tun da aka sami Najeriya a shekarar 1914, lokacin da aka haɗe kudu da arewa a matsayin Ƙasa ɗaya al’umma ɗaya.

Sannan ga kuma wata sabuwa da ke faruwa kamar yadda muka ji a makon da ya gabata cewa, wasu kafofin yaɗa labaran Ƙasar nan suka ruwaito labarin yadda wasu tsagerun ‘yan Ƙungiyar OPC masu rajin kare muradun Yarbawa suka yi barazanar yaƘi da Ƙungiyar Boko Haram a birnin Ikko. Haka nan a makon da ta gabatar ne muka ji ‘yan tsagerun yankin Neja-Delta suka yi tattaki da niyyar yin zanga-zanga a babban birnin tarayya Abuja, duk da jami’an tsaro sun yi nasarar datse su a garin Lakwaja, hedikwatar Jahar Kogi. Su ma ‘yan Ƙungiyar MOSSOB, masu fafutukar ganin Ƙasar Biyafara sun Ƙara nanata Ƙudurin su na ganin ko dai ɗan Ƙabilar Ibo a ba shi dama a shekara ta 2015 domin ya hau kujerar shugabancin Ƙasar nan ko kuwa a ba su dama su kafa Ƙasar su domin su cika burin jagoran su, Ojukwu da ya kwanta dama a kwanakin baya.

Duk ɗan Najeriya yasan da cewa, kullum ana Ƙara samun yawan aukuwar al’amura da suke nuna cewa, tsaro ya yi Ƙaranci a Ƙasar nan. Kama daga abin da ya shafi fashi da makami da fyaɗe da tashin bama-bamai da Ƙaruwar haɗura a kan manya da Ƙananan hanyoyi, da ma rikicin Ƙabilanci da na addini da ya Ƙi ci ya Ƙi cinyewa. Duk wannan ‘yan Najeriya na sane da su, kuma ana ta dogon turanci a kan yadda ya kamata waɗanda al’amarin ya shafa su fuskance shi. Idan ana son a yi maganin taɓarɓarewar tsaro a Najeriya, to, kuwa kamata ya yi gwamnati ta ɗauki mataki kamar haka.

Abu na farko, dole ne duk inda aka samu labarin fashi da makami ko fyaɗe ko daba ko kalare ko tashin bam ko faɗan Ƙabilanci ko na addini, garkuwa da mutane, fasa bututun mai, da ta’addancin tsagerun Neja Delta, OPC, MASSOB, Boko Haram. Tilas ne gwamnati ta kame waɗannan mutane kamar haka, na farko mai unguwa da kansila da dagaci da shugaban Ƙaramar hukuma da DPO na ‘yan sanda da daraktan ‘yan sanda na farin kaya na wannan Ƙaramar hukuma ko kuma yankin da abin ya faru. A kan cewa, tila su bada bayanin ya aka yi abin da ya faru wanda yake da alaƘa da tsaro ya auku, saboda duk al’amarin tsaron wannan yanki yana ƘarƘashin kulawarsu ne, saboda su ne wakilan hukuma ta wannan ɓangare a kuma wannan yanki.

Domin a matakin farko, waɗannan su ne waɗanda suke da haƘƘin kula da shiga da fitar mutane na yankin da suke ciki, wajibi ne gwamnati ta tuhume su a kan cewa, ko dai sun yi sakaci wani mugun mutum ko wasu miyagun mutane azzalumai sun zo da nufin cutar da al’umma, ko kuma da ma da haɗin bakinsu aka aikata dukkan ta’asar da ta auku. Tun da su ne suke shugabantar al’umma a wannan yanki duk abin da ya faru su ake tunkara.

Abu na biyu, wajibi ne gwamnati ta gudanar da bincike na gaggawa kuma bisa gaskiya da adalci kan dukkan rahotannin da suka shafi tsaro. Dole ne kuma a hukunta dukkan wanda aka kama da laifi komai girman muƘaminsa a kuma bayyana wa jama’a su ji. Sannan hukuma ta gargaɗi jami’anta a kan sakaci da aiki da kuma hukuncin duk wanda aka samu ya yi sakaci da aikinsa har aka samu ɓaraka ta gefensa.

Abu na gaba kuma, dole ne gwamnati ta samar wa jami’anta, ina nufin na tsaro cikakkun harkokin jin daɗi da walwalarsu da ta iyalansu. Tun daga kyakkyawan albashi da kuma kayan aiki waɗanda suka yi daidai da zamani, wanda wannan shi ne zai yi maganin cin hanci da rashawa a kan harkar tsaro.

Idan har gwamnati ta gwada ɗaukar waɗannan matakai al’amura ba su kyautata ba, to, tabbas kamar yadda masu magana ke cewa, da akwai lauje cikin naɗi, akwai waɗanda suke wa gwamnati zagon Ƙasa ta fuskar tsaro, akwai baragurbi, kuma dole gwamnati ta binciko su tare da hukunta su ko su wane ne, kuma komai girman muƘaminsu.

Domin mun yi imani dukkan wasu makamai ko na harbi ko masu fashewa da suke yawo a cikin Ƙasa gwamnati tana da masaniyar daga inda suka fito. Domin makami ba kamar abinci ba ne da ake shukawa a gona, haka kuma ba kamar kaya ba ne da kowane ɗan kasuwa zai iya sana’antawa a masana’antarsa, tabbas duk inda ka ga makami yana da alaƘa da hukuma ko ta kusa ko ta nesa domin yarjejeniyar mallakar makamai da Ƙasashen duniya suka cimma ta Kyoto da kuma ta Geneva ta tabbatar da haka. Ashe ka ga ke nan babu yadda za a ce hukuma ba ta da masaniyar yadda makamai suke yawo a cikin Ƙasa ko a hannun jami’anta ko a hannun ɗaiɗaikun mutane.

Idan kuwa aka bi dukkan waɗannan matakai al’amura ba su kyautata ba, to, tabbas gwamnatin da kanta ita ce kanwa uwar gami, kawai ana yaudarar al’ummar Ƙasa ne a kan sukurkucewar tsaro, amma da saninta aka yi wa sarari da harkokin tsaro don bai wa wasu da ma su ci karensu babu babbaka ala-bashi daga baya a cimma wata ɓoyayyar manufa. Daɗin daɗawa mun san cewa, al’amuran da suka shafi tsaro a kowace Ƙasa suna da buƘatar sirri, to, wajibin hukuma ne ta san irin dabarun da za a bi wajen kyautata al’amura da suka shafi sha’anin tsaro kuma suke da buƘatar sirri wanda mun san gwamnati tana nata ƘoƘarin. Mun san akwai dokar da gwamnati ta sanya wa hannu kwanakin baya ta ‘yancin neman bayanai wato ‘Freedom of information Bill’, mun san da cewa, duk inda mutum ya kai ga neman labarai ba zai binciki ya ake gwamnati take da makamai ba kuma nawa aka saya, nawa aka ɓatar.

Mun san da cewa, duk wani makami da yake a Najeriya idan ba na gwamnati ba ne wanda ita ke da alhakin mallakarsa da kuma kulawa da shi, kuma babu ta yadda za a yi ya fita ba tare da masaniyar waɗanda abin ya shafa ba. To, kuwa babu ta yadda za mu yarda cewa, makamin nan ba shigo da shi aka yi ko dai takan iyaka ko kuma ta gaɓar teku ko ta amfani da jirgin sama wanda duk waɗannan wurare alhakin gwamnati ne ta kula da su, idan kuwa ta yi sakaci da wannan ɓangare, to, tabbas wannan kowace irin gwamnati ce ba ta cancanci a ci gaba da ba ta goyon baya ba, tun da ba ta iya tsare wa al’umma Ƙasa ta fuskar tsaro ba. Haka kuma babu wani mutum da zai iya Ƙera makami ba tare da gwamnati tana da masaniya ba, domin dukkan wani abu da ya shafi tsaro babu wanda yake da Ƙarfin iko a kansa sama da hukuma.

Kamar yadda muka ji cewa hukumomi na ƘoƘarin sanya na’urar binciken a Ƙofar shiga majalisa mai gani har hanji wadda ake kira ‘Fulbody scanner’ don kare ‘yan majalisa. To, su ma al’ummar Ƙasa suna buƘatar wannan na’ura don kare rayuwarsu da dukiyarsu, domin ‘yan majalisa ba su kaɗai ba ne ‘yan Najeriya ba, mu ma talakawa muna da haƘƘin gwamnati ta kula da mu ta dukkan ɓangarori ba sai ta fuskar tsaro ba kawai.

Kuma bisa yadda muka ji shugaban Ƙasa ya gabatar a cikin kasafin kuɗin shekarar nan mai kamawa an ware kuɗi kusan Naira biliyan 921.91 a sha’anin tsaro muna fatar al’amura su kyautata wanda a cikin wannan halin ne abin takaici za ka iske ba wanda suka fi cutuwa da rashin tsaro da mummunan talauci da rashin aikin yi da rashin haɗin kai da shugabanci irin al’ummar arewacin Najeriya.

Lallai muna kira ga gwamnati ta yi iyakar iyawarta wajen kawo Ƙarshen tashin bama-bamai da kuma rikicin Ƙabilanci da na addini da ya Ƙi ci yaƘi cinyewa a birnin Jos da sauran sassan Jahar Filato da garkuwa da mutane da fyaɗe da satar jarirai a asibitoci da satar mutane a kan hanya da rikicin manoma da makiyaya da waɗannan maƘudan kuɗaɗen da aka fitar wajen sha’anin tsaro.

Idan ba haka ba kuwa, abin da Bahaushe yake cewa, abin da ya ci doma ba zai bar awe ba. Wanda wannan yake nuna irin juyin juya halin da yake faruwa yanzu haka a yankin tsibirin Larabawa da Arewacin Afirka babu abin da zai hana shi wanzuwa a Najeriya, kamar yadda muka ji kwamitin da shugaban Ƙasa ya kafa kan rikicin bayan zaɓe ƘarƘashin jagorancin dattijo Sheikh Ahmad Lemu, sun yi gargaɗi a kan wannan batu. Lallai hukumomi su sani duk waɗancan abin da suke faruwa a yankin Ƙasashen Larabawa rashin adalci ya janyo shi, don haka adalci shi ne zai zaunar da Ƙasar nan lafiya, kuma shi ne zai ci gaba da zaunar da Ƙasar nan a matsayin Ƙasa ɗaya al’umma ɗaya. Muna tabbatar wa da gwamnati kamar yadda suka sani yanzu duniya tana tafiya ne bai ɗaya. Allah ya taimaki Ƙasar mu Najeriya, ya ba mu lafiya da zama lafiya.

Yasir Ramadan Gwale, yasirramadangwale@hotmail.com

http://yasirramadangwale.blpgspot.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.