Yajin Aikin Ma’aikatan Ƙananan Hukumomin Filato: NLC Ta Ba Gwamna Jang Wa’adin Kwanaki 10

0
1012

Isah Ahmed, Daga Jos
A Igabada   dambarwa da ake yi tsakanin gwamnatin Jahar Filato da ma’aikatan Ƙananan hukumomin jahar kan yajin aikin da suke yi na tsawon watanni bakwai, kan a biya su sabon tsarin albashi na Naira dubu sha takwas. Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwadago ta Jahar Filato ta ɗebar wa gwamnan jahar, Jonah Jang wa’adin kwanaki goma ya warware wannan matsala, ko kuma gabaki ɗayan ma’aikatan jahar da sauran kamfanoni masu zaman kansu da ke jahar su tafi yajin aiki tare da zanga-zanga kan wannan al’amari.

Shugaban Ƙungiyar Ƙwadagon ta Jahar Filato, Kwamared Jibrin Bancir ne ya bayyana haka, a wani taron ‘yan jarida da Ƙungiyar ta kira a cibiyar ‘yan jarida da ke garin Jos.

Shugaban Ƙungiyar Ƙwadagon ya ci gaba da cewa, sun yi wannan matsaya ne, ganin yadda gwamnan ya Ƙi warware wannan matsala. Ya ce a maimakon gwamnan ya tsaya ya warware wannan matsala, sai ya ɓuge da zargin cewa, wai abokan adawarsa ne suke amfani da ma’aikatan.

Ya ce a taron da gwamnan ya yi da masu ruwa da tsaki na jahar kan wannan matsala, gwamnan ya bayyana wannan zargi da yake yi wa ma’aikatan.

Har ila yau, ya ce a lokacin da ministan yaɗa labarai ya kai ziyara a jahar, gwamnan ya sake irin wannan zargi. Shugaban Ƙwadagon ya Ƙalubalanci Gwamna Jang kan ya fito da shaidar cewa, abokan adawarsa suna amfani da ma’aikatan.

Ya yi kira ga gwamnatin Jahar ta Filato ta duba irin mawuyacin halin da ma’aikata da sauran al’ummar jahar suka shiga, sakamakon yajin aiki. Ya ce mu dai Ƙofarmu a buɗe take wajen ganin an zauna an sasanta wannan matsala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.