Gwamna Mukhtar Ramalan Yero: Kainuwa Dashen Allah!

1
2083

SHA’ANIN Allah ba ya buƙatar tambaya saboda ikonSa ya zarce tunani ko wani hangen nesa, komai naShi ne ba ya buƙatar komai a wurin wani. Dukkanin halittun da ya yi, ya ajiye masu lokacin komai manufa ta fannin arziƙi, muƙami, aure, ɗaukaka, rinjaya, ilimi, basira, hankali, da kuma ajali wato mutuwa wadda tabbas ce ga dukkanin halitta. Saboda haka ashe jahilci ne da rashin tunani ke sanya mu hassada a kan wata dama ko wani abu da Allah ya baiwa wani/wata a rayuwarsa/ta hasali ma akwai wannan abin cikin abubuwa da aka rubuta zai/za ta yi a rayuwarsa/ta. Hassada kuwa guba ce ga zuciya tare da jiki, kuma ba ta hana abin da Allah ya tsara wa bawanSa, illa ta ƙara sanya shi a gaban masu yi masa hassada, kuma komai dogon lokacin da aka ɗauka sai ya shiga gabansu da rana tsaka.

Garin Zariya yana ɗaya daga cikin gidajen sadaukai kuma jaruman da suka tabbatar da jihadin Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo da ɗansa Muhammadu Bello, gida ne na mayaƙa kuma masu ilimi na zamani a yau da kuma na Islamiyya wanda cikin jininsu yake tun asali. Hasali ma saboda ilimin Islamiyya ake yi wa garin laɓabin ‘Birnin Ilimi’, a wannan gari mai ɗimbin tarihi aka yi Sarki Jafaru wanda ke ayyuka uku a kowace rana ta Lillahi, Shi ne Sarki kuma Liman sannan kuma Alƙali, hasali ma a wurinsa sarakuna suka samo aikin alƙalanci na shiga tsakani ko tsakanin mata da miji ko iyaye da ‘ya’yansu ko makamantan haka sai idan abin ya faskara ake neman ƙuliya.

Unguwar Ƙaura da jin sunan ka san gidan jarumai ne waɗanda suke kasancewa sahun gaba wajen yaƙi a can da, yanzu kuma sun haɗa yaƙi da mulki, wannan unguwa mai karatu nan ne aka haifi Ɗan Autan Gwamnonin Najeriya, Alhaji (Dokta) Mukhtar Ramalan Yero wato sabon Gwamnan tsakiyar Najeriya a taƙaice Jahar Kaduna, bayan mutuwar Sa Patrick Ibrahim Yakowa kwanan baya. Mutane da dama da na zanta da su dangane da sabon angon Hajiya Kaduna sun bayyana cewa, shi ruwa ne masu aiki sannu, haka kuma idan zai yi magana ya kan yi tunani da duban abin da zai je ya dawo, manufa yana da hangen nesa, haka kuma yana da ilimi na zamani da Islamiyya. Hasali ma shi ƙwararre ne a fannin abin da ya shafi kuɗi, abin da ya karanta ke nan kuma nan ne gonarsa. Na samu saninsa a lokacin ina aiki da Jaridar Turanci ta ‘Companion’, a lokacin da ni da Abdullahi Isa wanda a yanzu yake aiki da sashen Hausa na BBC muka je ganin Alhaji Namadi Sambo a lokacin da yake takarar muƙamin gwamnan Jahar Kaduna domin tattaunawa da shi. To, a can ne muka haɗu da shi Gwamna Mukhtar ya karɓe mu da ladabi da kuma ƙauna tamkar mun jima da sanin juna, kuma tun daga wannan lokaci yake girmama ni. Sunansa ya fito fili ne a lokacin da aka ba shi muƙamin Kwamishinan Kuɗi lokacin da Mazayyani Namadi Sambo yake Gwamnan Jahar Kaduna, a wannan lokacin ya fito da iliminsa domin ganin ya ba da tashi gudunmawa, da yake mutum ne mai son wasanni musamman na motsa jiki tare da ganin matasa sun sami dogaro, sai ya yi amfani da wannan lokaci wajen fito da shirye-shiryen da za su sanya matasa su daina ɗaukar doka a hannunsu, hasali ma yana cikin waɗanda su ka yi suna wajen shirya gasa ta ƙwallon ƙafa da makamantan haka a tsakanin ƙungiyoyin matasa domin sanya rayuwarsu a turba mai kyau domin su bada tasu gudunmawa kamar yadda ya kamata.

A wani bayani kuma duk da yake baya son a faɗa, wata majiya ta nuna mini cewa, yana da wata gidauniya ta ɓoye da yake taimaka wa matasa musamman masu ƙaramin ƙarfi domin karatu da kuma sana’o’in hannu tun da aikin gwamnati ya yi ƙamshin ɗan goma a wannan lokaci ga ‘ya’yan masu hannu da shuni balle ‘ya’yan talakawa waɗanda suka kasance gugar yasa. Haka ya ci gaba da kasancewa har lokacin da aka ba shi muƙamin Mataimakin Gwamna a lokacin da Mazayyani Namadi Sambo ya zama Mataimakin Shugaban Ƙasa bayan rasuwar Alhaji Umaru Musa ‘Yar’Aduwa, Allah ya jiƙansa da gafara, amin.

Haƙurinsa da ladabinsa da kuma tunaninsa tare da jarumtakarsa suka taimaka masa ƙwarai wajen jure dukkanin wani abin da ya zo masa, amma duk da irin yanayin da ya samun kansa na raɗaɗin mulki ba ka iya ganewa a fuskarsa saboda shi mutum ne mai zurfin ciki. A lokacin da yake mataimakin gwamna ya riƙe muƙamai da dama, amma babu wanda ake yabonsa dangane da shi sai muƙamin jagorancin alhazzan Jahar Kaduna zuwa ƙasar Makkah saboda a wannan lokaci mutanen da suke yi masa kallon kifin rijiya sun sha mamaki ƙwarai ganin irin ɗimbin nasarorin da aka samu, hasali ma hukumar alhazzan ta jima ba ta samu irin waɗannan nasarorin ba. Haka kuma a lokacin da yake wannan muƙami ya taka muhimmiyar rawa wajen ayyukan matasa tare da bayar da gudunmawa domin ganin an samu zaman lafiya tsakanin ƙabilu daban-daban na Jahar Kaduna ko ta hanyar bayar da kofuna domin a yi gasa ko kuma ta wasu hanyoyi masu kama da haka, duk kuwa da barazana tare da rashin tabbas da ya kasance a ciki a hannun ‘yan lelen tsohuwar gwamnatin Yakowa, amma saboda saninsa ne cewa, komai nisan jifa ƙasa za ta je, ya zura masu na mujiya kurum.  Ranar Asabar 15/12/12 rana ce da ta shiga cikin tarihin Jahar Kaduna da Najeriya baki ɗaya saboda a wannan ranar ce Allah ya karɓi rayuwar wasu al’ummomi cikinsu kuwa har da tsohon gwamnan Jahar Kaduna, Sa Patrick Ibrahim Yakowa wanda mutuwarsa ta girgiza jahar da ƙasa baki ɗaya saboda ko ba komai ta zama darasi ga ‘yan Adam domin su gane cewa ‘Mutum duka tara yake bai cika goma ba’, ban san baɗinin Yakowa ba. Amma a zahiri ya yi ayyuka da dama da za a jima ana tuna su kamar titin Rigasa da tagwayen hanyoyi da za su haɗu da Matatar Man Fetur ta ƙasa da cikin garin Kaduna da ginin gadar da ta haɗa yankin Kudanci da Arewacin garin Kaduna, ya kuma yi wasu abubuwa da nufin kawo fahimtar juna tsakanin al’ummomin daban-daban da ke jahar.

Bayan mutuwarsa ne, aka naɗa Alhaji Mukhtar Ramalan Yero a matsayin Gwamnan Jahar Kaduna, zancensa na farko shi ne zai ɗora inda Yakowa ya tsaya kuma yana buƙatar haɗin kan kowa domin ya sauke nauyin da ke kansa tare da ganin ya cika alƙawuran da suka yi wa al’ummomin jahar lokacin da suke neman ƙuri’unsu a can baya. Ya kuwa soma ne da biyan kuɗaɗen hutu na ma’aikatan jahar da tsohon gwamnan ya yi alƙawari cewa, zai biya kafin bikin Kirismeti. Mai karatu ba sai na faɗa ba akwai namijin aiki a gaban wannan matashi saboda kasancewarsa tamkar wanda ya auri mashahurriyar matar da ta rasa miji. Matar kuma ta shahara a fannin mulki da ilimi da dukiya da siyasa da kuma ‘ya’ya masu hikimomi a kowane mataki na rayuwa, balle kuma Jahar Kaduna gidan mutanen Arewa, gidan siyasa da mulki da ilimi kowane iri, gida ga duk wani ɗan ƙasa da ke ganin ya isa, tashar sojoji manya da ƙanana, mazauni kuma cibiyar sarakuna, jahar da kowane addini ke bugun gaban tashi ce ko yana da yawan mabiya, Jahar da ko Romawa ba su nuna mata yawan Majami’u, haka kuma Indonesiya ba ta gwada mata yawan Masallatai manya da ƙanana, cibiyar kowace irin haja kuma gidan noma da kiwon dabbobi, saboda yanayin zafin mulkinta da sha’anin gudanar da al’amuranta ake ganinta tamkar ƙaramar Najeriya, saboda kasancewarta gida ga kowane jinsi da ke Afirka ta Yamma.

Wannan jaha mai waɗannan ababe ne Allah cikin ikonSa ya bai wa Dokta Yero jagorancinta, a daidai wannan lokaci da Najeriya ke cikin yanayi na rashin tabbas a fannoni daban-daban. Ko baya ga irin yanayin mulkin jahar da yake ɗauke da ƙalubaloli iri daban-daban, to da akwai kuma matsaloli da dama da kowa ke son ganin sabon gwamnan ya kawar cikin wannan ƙanƙanin lokaci ganin cewa, a shekarar 2014 za a soma shirin zaɓe domin samar da sababbin shugabanni a matakin shugaban ƙasa da gwamnoni da kuma ‘yan majalisun dokoki na tarayya da jahohi. Wani abin kuma da shi sabon angon Hajiya Kaduna ke ciki shi ne samar da alƙibla ga sababbin shugabannin ƙananan hukumomi 23 da aka zaɓa a farkon wannan wata waɗanda ba su jima da kammala ɗaukar horo ba domin kama aiki. Haka kuma akwai ɗimbin ayyukan raya ƙasa da wasu an kammala, wasu ana kan yi wasu kuma za a soma a kowane saƙo na jahar da kuma wasu da ake son a aiwatar ganin tsohuwar gwamnatin ba ta yi wasu ayyuka masu yawa ba, saboda barazanar rashin tsaro da rikicin zubar da jini da ya yi ta faruwa a lokuta da dama.

Wani abin da kuma ake neman bakin zarensa a jahar shi ne talauci wanda a kullum ƙaruwa yake yi saboda rashin ayyukan yi tsakanin matasa maza da mata, wannan kuwa ba ƙaramin musiba ba ce, ganin yadda ɗimbin matasa suka koma maroƙa ko kuma mashaya domin kawai su burge ‘yan siyasa. Rahotanni masu cin karo da juna na nuna cewa, lokaci ya yi da ya kamata gwamnati ta cire ra’ayin siyasa ta fitowa da ɗimbin matasan jahar da cibiyoyin sana’o’in hannu a kowane saƙo na jahar, haka kuma ta canza shawara a kan zancen hana sana’ar acaɓa da ake zargin za a yi a cikin sabuwar shekara, a maimakon haka a fito da shirin yi masu rajista domin saninsu tare da yi masu horo da zai sanya su, gudanar da sana’o’insu a ƙarƙashin doka, domin su daina ɗaukar doka a hannunsu.

Wani abin kuma da ya kamata gwamnati ta yi, shi ne gyaran wurin koyon sana’o’in naƙasassu tare da wadata shi da kayayyakin aiki domin ba su horo tare da tallafi idan sun kammala su sami dogaro mai amfanin rayuwarsu maimakon gararaba a kan titunan motoci. Ya kuma kamata ma’aikatar mata ta samar wa mata masu yawo a ofisoshin gwamnati sana’o’in hannu domin su samu dogaro mai amfanin rayuwarsu, yin haka kamar ba su tukwici ne dangane da rawar da suka taka a lokutan zaɓuɓɓukan da suka gabata.

Domin bunƙasa Jahar Kaduna da abinci da wasu ababe da ke ƙara kaurin kuɗi ga gwamnati, ya kamata a gyara madatsun ruwa da a halin ke fuskantar barazana da ya sanya suka kasance haɗari ga rayuwar mutane da ke kusa da su a lokacin damina, matasa kuma da a da can ke himmatuwa wajen noman rani tare da abin dogaro, a yau su ne sahun gaba wajen aikin tayar da zaune tsaye da wasu marasa kishin ƙasa ke sanya su domin biyan wata buƙata ta kawunansu. Ya kamata gwamnati ta sake tunani wajen gyaran su waɗannan madatsun ruwa tunda ko ba komai suna samar da ayyukan yi ga ɗimbin matasa a birane da karkara, madatsun sun haɗa da ta Kajuru da Matari da kuma ta Birnin-Gwari.

Haka kuma lokaci ya yi da gwamnati za ta yi amfani da wuraren yawon shaƙatarwa, ta domin samun kuɗaɗen shiga ƙari ga abin da jahar ke samu daga aljihun gwamnatin tarayya. Ya kamata a samar da gidan tarihi da sunan jaruma Amina a garin Turunku da ke ƙaramar hukumar Igabi, bai kamata a bar waɗannan kayayyakin tarihin su lalace ga banza ba, za a samu kuɗaɗen shiga masu tarin yawa ko baya ga samun cibiyar tarihi ga ɗaliban jami’o’in ƙasar nan. Wasu wuraren shaƙatawa sun haɗa da inda ruwa ke tsiyaya a garin Kafanchan da wasu wurare a garin Ƙaura da ke canzawa sai ka ɗauka kana ƙasashen Turawa ne da kuma sauran gidajen tarihi da ke wurare da dama ciki kuwa har da garin Kagoro da Nok da wasu da dama.

Sai kuma ‘yan siyasa waɗanda ya kamata su haɗa kawunansu wuri ɗaya domin ba da gudunmawar da za ta samar da ɗimbin nasarorin da ake buƙata domin ganin jahar ta kasance cikin yanayin da ya kamata, ta hanyar kauce wa duk abin da ke kawo fitina ko ka-ce-na-ce a tsakanin al’umma. Gwamnati kuma ta samo wa su ‘yan siyasa matsuguni a cikin wannan tafiya domin ta ji daɗin tafiyar da lamuranta domin ciyar da jahar gaba a kowane ɓangare. Lokaci ya yi da gwamnatin Yero za ta dawo da gidajen da gwamnatin su Maƙarfi suka samar a wurare da dama ciki da wajen babban birnin jaha domin kwantar da kowace irin barazana ta rikici da ababen da suka yi kama da haka.

A fannin ilimin yara tun daga ƙaramar makaranta zuwa manya, ya kamata gwamnati ta haɗa hannu da shugabannin ƙananan hukumomi domin kaiwa makarantun da iska ko ruwan sama ya yi wa gyara ɗaukin da ya kamace su, tare kuma da samar masu da kayayyakin aiki domin ɗaliban da ke karatu a cikinsu, su kasance cikin yanayin da ya kamata. Haka kuma a samar da magunguna a farashi mai sauƙi a asibitoci manya da ƙanana musamman a karkara domin rage wa talakawa wahalolin da suke cin karo da su idan ba su da lafiya ko kuma mata masu juna biyu da ke haɗuwa da matsaloli sakamakon rashin wadataccen magani ko kayan aiki ko kuma isassun ma’aikata a karkara. Su kuwa al’ummomin Jahar Kaduna ya kamata su mance da bambance-bambancen da ke tsakaninsu domin ganin sun bada ta su gudunmawa domin ginin sabuwar jaha inda za a samu walwala da zaman lafiyar da zai haifar da ci gaba a kowane mataki na rayuwa. Za su iya yin haka ta hanyoyi da dama, cikinsu har da zancen biyan kuɗaɗen haraji domin tallafa wa gwamnati ta hanyar samun ƙarin kuɗin shiga masu ƙauri da za su taimaka domin gudanar da ayyukan raya ƙasa a kowane mataki, na biyu mutane za su bada gudunmawa ta hanyar kauce wa yaɗa jita-jita a tsakaninsu wanda ke kawo fitina da take haifar da rashin tabbas tsakanin al’umma, na uku kuma yanzu lokacin hunturu ne saboda haka su dawo rakiyar ƙona daji domin kauce wa tashin gobara, na huɗu kuma shi ne kai rahoton duk mutumin da ba su yarda da al’amuransa ba ga hukumomin da abin ya shafa, haka kuma su kasance masu bin doka da oda domin kaucewa fushin hukuma. Allah ya yi wa sabon angon Jahar Kaduna, Dokta Mukhtar Ramalan Yero jagora domin ya samar da ɗimbin nasarorin da za su kai Jahar Kaduna tudun mun tsira, amin.

 

Alkammawa, ya rubuto daga Unguwar Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, 07030399110 Birnin Gwamna Kaduna, alkammawa2000@yahoo.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.