Gwamnatin Jigawa Ta Kasafta Naira Biliyan 115 Na 2013

0
758

JABIRU A HASSAN, Daga Dutse

GWAMNAN Jahar Jigawa, Dokta Sule Lamiɗo ya gabatar da kasafin kuɗin shekara ta 2013 ga majalisar dokokin jahar na Naira biliyan 115 ranar Litinin ɗin da ta gabata domin amincewar majalisar kamar yadda aka saba.

An dai sami ƙarin kashi 5 na kasafin kuɗin kan kasafin kuɗin shekara ta 2012, kuma za a kashe kashi 56 na kasafin kuɗin wajen ayyukan samar da ababen more rayuwa ga al’ummar Jahar Jigawa.

Gwamna Sule Lamiɗo ya  nemi majalisar da ta amince da wannan kasafin kuɗi ta yadda gwamnati za ta sami damar ci gaba da gudanar da aikace-aikace ga al’umma ba tare da tsaiko ba.

Da yake mayar da jawabi, shugaban majalisar dokokin, Alhaji Adamu Ahmed Sarawa ya tabbatar wa da gwamnan cewa, majalisar dokokin za ta gaggauta duba wannan kasafin kuɗi domin amincewa da shi domin gwamnati ta sami ikon aiwatar da kyawawan manufofinta na bunƙasa Jahar Jigawa.

Sannan kakakin majalisar ya jinjina wa Gwamna Sule Lamiɗo saboda ƙoƙarin da yake yi na ciyar da Jahar Jigawa gaba kuma bisa sarrafa dukiyar jahar cikin sanin ya kamata, inda daga ƙarshe shugaban majalisar dokokin ya buƙaci ɗaukacin al’ummar Jahar Jigawa da su ci gaba da bai wa gwamnatin ta Dokta Sule Lamiɗo haɗin kai da goyon baya.

A wani ci gaban kuma, Alhaji Adamu Ahmed Sarawa ya jaddada cewa, majalisar  dokokin Jahar Jigawa tana goyon bayan Gwamna Lamiɗo ya fito takarar shugabancin Najeriya a shekara ta 2015 domin sun haƙiƙance cewa, ƙasar nan za ta sami ci gaban da bata taɓa mafarkin samu ba idan Dokta Sule Lamiɗo ya zamo jagora.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.