Jana’izar Azazi: An Motsa Gashin Baki Tsakanin Shugaban Ƙasa Da Akibishop Ogbebor

0
1054

AHMAD ABDUL, Daga Kalaba

AN motsa gashin baki a bikin bizne gawar Janar Anderw Azazi (ritaya) tsohon mai baiwa shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan shawara kan harkokin tsaro wanda ya rasu sanadiyyar haɗarin jirgin sama mai sauƙar ungulu wato Helicopter a Nembe, Yenagoa, Jahar Bayelsa kwanan baya tsakanin babban limamin cocin Bomadi da ke Jahar Delta, Akibishop Hyacinth Ogbebor da shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a wajen jana’iza.

A huɗubar da Akibishop Ogbebor na Bomadi ya gabatar wajen jana’izar, ya ɗora alhakin koma baya da Jahar Bayelsa halin yanzu take fama da shi da cewa, “har yanzu an kasa gyara mana babbar hanyar East-West muna fama da samun labarin yawaitar haɗuran motoci da suke laƙume rayukan jama’a.

“Ya ci gaba da cewa, ‘harkokin gwamnati sun taɓarɓare a ƙasar nan cin hanci da rashawa ya yi katutu ya samu gindin zama a ƙasar nan”, al’amarin da Akibishop ya ce dole sai gwamnati ta tashi tsaye wajen magance waɗannan matsaloli.

Da ya juya kan hanyar Bayelsa zuwa Fatakwal, Akibishop Ogbebor ya nemi shugaban ƙasar da “a gyara mana hanyar East-West”. Ya ce kusan kowace rana ta Allah ana samun rahotannin haɗarin manyan motocin ɗaukar mai da ke faɗuwa suna haddasa asarar rayuka.

Don haka ina roƙon a gyara mana wannan hanya ta yadda “idan na taso daga Bomadi, Jahar Delta zan zo Yenagoa ba ta sama zan tashi in bi ba”. Da yake tsokaci game da irin haɗuran jiragen sama da na helikopta, babban limamin cocin ya bayyana ƙarara gwamnati ta gaza wajen magance haɗuran jirage a ƙasar nan.

“Idan da ana kula da ɗaukar matakin kare aukuwar matsalar da Azazi da Yakowa ba su mutu ba a haɗarin jirgin, don haka akwai ayar tambaya a wannan gwamnati na kare haƙƙin talaka da muradinsa, inji shi. Ya ci gaba da cewa, a tsarin aikin gwamnati ana bin cancanta da ƙa’ida amma yanzu alfarma da biyan buƙatun magoya bayan ‘yan siyasa ya yi yawa, an daina bin ƙa’idar cancanta da ƙa’idar ɗaukar ma’aikaci.

Da yake mayar da martani tare da kare gwamnatinsa, shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya ce halin da ƙasar nan ta tsinci kanta gyara ta “kisan baƙi ne sai gayya don haka akwai buƙatar kowane dan r nan ba ɓata wa juna suna ba”, Najeriya ya bayar da gudunmawarsa wajen gyara ƙasa ba ruguguwar ɓata wa juna suna ba.

Daga nan shugaban ƙasar ya ci gaba da cewa, “ba daidai ba ne a ɗora wa mutum guda laifin lalacewar al’amura ba, a’a, kamata ya yi a yi wa juna adalci, matsala ce ta taru, a faɗa wa juna gaskiya, a haɗa hannu ƙarfi da ƙarfe a gyara ƙasa.

Game da cin hanci da rashawa, shugaban ƙasa ya bayar da tabbacin magance hakan nan gaba sai tarihi a ƙasar nan domin cimma buri akwai buƙatar kowane ɗan ƙasa ya bada tasa gudunmawa wajen kawo ƙarshe, matsalolin da take fuskanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.