masu hikima sun ce

0
437

ANA haɗa haɗuwa na addini da na jini da na maƙwabtaka a ce sun yi daidai, sai in ba a gane ba.

Addinin Allah Ya sami karɓuwa ne musamman a ƙasar nan da ƙasashen da ya tsira ta maƙwabtaka ba da yaƙi ko iyaye su tilasta wa ɗan su ba.

Idan an tilasta wa mutum shiga addini, to, ta yaya za a tilasta shi zuwa yaƙi ya fi son sa ba ransa ba.

Ko gobe ga masu hankali ba sai an je lahira ba, duk yadda ilimin zamani ya kai da daɗi, ashe na addini bai fi shi ba?

Komai daɗin abin da za ya ƙare, ina bambancinsa da rashinsa wahalar da za ta ƙare ashe ba ta fi su ba? Ba a dai samun abin da Allah sai an bi shi, shi ne ka bauta maSa, da bin umarninSa ne ake samun ɗaukakar addini wanda ya fi komai a nan duniya, da shi ne kuma ake samun rabon lahira da waninSa ba.

Me ya sa an san cewa, komai na Allah ne kuma ana yarda Ya fifita lahira a kan duniya, kuma Ya yi mana kyauta da duniya, lahira ce ya ce mu nema, sai ba a damu da masu neman lahirar ba, ko da kuwa sun haɗa da neman rabon su na duniya sai aka ƙi son abin da suke so da Allah Ya fi so, alhali an san shi ne Ya ba mu abin da duk muke da shi, amma waɗanda suka sa duniya gaba ana yi masu komai da suke so, ko da sun yi waɗannan ba a cika son faɗi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.