Muhimmancin Kyautata Wa Iyaye

1
2081

BABBAN abu muhimmi daga cikin kyautata wa iyaye shi ne yin biyayya a gare su cikin kowane irin al’amari musamman wanda bai keta ƙa’idar addinin Musulunci ba. Wannan kuwa shi ne aiwatar da duk wani umarni da za su bada na yi ko na bari, lallai a yi biyayya a cikinsa.

Haka kuma a riƙa neman shawara a wajen iyaye tare da yardarsu kafin zartar da muhimman al’amurra nasu. Kada ya ɓata masu rai, kada ya riƙa ɗaga murya sama da tasu idan suna magana balle har ya yi masu tsawa. Kada ya riƙa ɓata rai tare da murtuke masu fuska balle kuma ya yi fushi da su.

Ya kasance mai sauƙin kai da walwala a gabansu tare da yi masu tambaya a kan abin da bai sani ba, wanda yake tunani sun fi shi ilimi a kansa, amma idan ya lura ba su da ilimin abin, to, bai kamata ma ya tambaye su ba.

Kuma wajibi ne ɗa ya ba iyayensa kyakkyawar kula ta fuskar samar masu da abinci da tufafi masu kyau tare da ingantaccen wurin kwana.  Kada ya guje su musamman a lokacin da suka tsufa.  Kuma haramun ne ɗa ya riƙa yi wa iyayensa tsaki ko buga masu tsawa idan sun umarce shi, ya yi masu wani abu, muddin bai saɓa wa shari’ar Musulunci ba, kai ko da ma ya saɓa, haramun ne ga ɗan ya yi haka, don akwai hanyar da ya kamata ya yi don tausasa su cikin ruwan sanyi.

Kuma idan iyaye suka umarci ɗa da yin abin da ya saɓa wa shari’a, ba tawaye zai yi masu ba, sai ya lallashe su tare da jan hankalinsu cikin murya mai sanyi. To, idan suka ƙi, suka turje, to, ba zai yi masu biyayya ba. Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce: “Kuma mun yi wa mutum wasiyya da cewa ya kyautata wa iyayensa kuma idan suka yi jayayya da shi a kan ya saɓa wa dokar Allah, to, kada ya yi masu biyayya. A cikin wannan makomarku zuwa gareNi take…” Q29:

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.