Yadda Ake Yin Adalci A Tsakanin Mata

0
2082

Wannan kalma ta “Adalci”, a kodayaushe ma’anarta guda ɗaya ce. ita ce kuwa ɗora abu ko ajiye shi ko kuma bayar da shi a inda ya cancanta ko ya dace.  Kuma ana iya fassara ta da cewa, bayar da haƙƙi ga mai shi ba tare da ragi ko ƙari. To, idan aka yi ƙari, to, wannan ƙarin shi ne ake kira kyautatawa.  Amma idan aka rage wani abu daga ciki, to, ragewar ita ake kira zalunci.

To, duk da yake haka ma’anar adalci take kamar yadda na bayyana, to, yadda ake tabbatar da adalci a tsakanin mata, yana da tsawon gaske, amma a taƙaice tsayar da adalci a tsakanin mata yana samuwa ne ta hanyar yi wa kowace daga cikinsu ɗawainiya gwargwadon buƙatarta bisa tsarin shari’a, musamman ta fuskar abinci da tufafi, kuma daidaita masu rabon kwana.

Misali, wata matar takan ci abinci kaɗan ne kawai, wata kuwa ba ta ƙoshi sai ta ci da yawa.  Haka nan kuma wata ba ta da jiki sosai don haka yadi kaɗan zai wadace ta yin sutura, wata kuwa tana da jiki wato mai ƙiba ce, don haka sai ta yi amfani da yadi mai yawa.  To, dole ne kowace daga cikinsu a ba ta gwargwadon buƙatarta.

Shi kuwa rabon kwana idan namiji yana da mata fiye da ɗaya a tsakaninsu (su matan) za su shirya rabon kwana.  Misali, idan ya kwana biyu a ɗakin Uwargida, haka zai yi a ɗakin amarya, wannan shi ne adalci. Amma akwai waɗansu abubuwa da ba za a iya daidaitawa ba, misali kamar fifikon kyautata masa ko fifikon daɗin saduwa ko iya girki da makamantan haka.

Haka abin yake a ɓangaren soyayya da sumba don ba ya yiwuwa a tabbatar da adalci a irin waɗannan abubuwa. Amma idan har hakan ta kasance bai kyautu namiji ya nuna haka a fili har a gane ba, sai ya bar shi a matsayin sirri.

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce, “kuma ba za ku iya tabbatar da adalci (gaba ɗayansa) a tsakanin mata ba ko da kun so yin haka ɗin, to amma kada ku karkata dukkan karkata ku bar ɗayar kamar wata ratayayya, to, amma idan kuka gyara kuma kuka ji tsoron Allah, to, lallai ne Allah Ya kasance Mai yawan Gafara Mai jinƙai. 4:129.

Kuma dai yana daga cikin adalci a tsakanin mata a ba kowace irin abincin da ta saba ci da irin tufafin da take ɗaurawa a gidansu. To amma idan mafificiya ce daga cikinsu ta yi rangwame a kan haƙƙinta, to, ta kyauta sai daidaita su a tsayu a tsakiya.  Ɗayar ta ci arziƙin gudar. Imam Malik ma yana da ra’ayin haka, har ma yana cewa, daidaita su ɗin kuma shi ya fi soyuwa a garemu”. Amma fa bisa ruwaya mafificiya, duk abin da aka yi wa wancan ita ma sai a yi mata.  Amma waɗansu malamai sun bambanta a kan wannan magana, bisa hujjar cewa, ai ba da abincin gidansu aka ce a ciyar da su ba amma na gidan mijin aka ce a ciyar da su, kenan iyakar ƙarfin mai gidan za a duba.  Allah Ne mafi sani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.