Gwajo-Gwajo: Nagari Na Kowa.

0
1828

TUN komawar Ƙasar Najeriya bisa tafarkin mulkin dimokuraɗiyya shekaru sha uku ke nan da suka gabata, an sami sababbin jini da al’ummominsu suka zaɓe su domin su shugabance su ko wakiltarsu a muƘamai iri daban-daban wato a matakin Ƙananan hukumomi, jahohi ko kuma a gwamnatin tarayya. Da yawa bayan an zaɓe su kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba, domin mafi yawansu an yi zaɓen tumun-dare ne. Da yawa al’umma na kokuwa da turin mota da suke yi wa ‘yan siyasa masu halayen Ɗantsako samu ka Ƙi dangi da masu hali irin na Kura daga ke sai ‘ya’yanki. Akwai wasu kuwa masu hali irin na tururuwa in ban da su tara ba ci ba sha, babu abin da suka sani.

Da yake dai shi mulkin dimokuraɗiyya ya ba talakawa ‘yanci duk bayan wani lokaci suna iya amfani da Ƙarfin Ƙuri’arsu domin canza miyagun shugabannin da suka yi kuskuren zaɓe domin maye su da nagari.

Duk da cewar, ‘yan siyasa sun yi Ƙaurin sunan rashin cika alƘawari amma ba su taru suka zama ɗaya ba, domin akwai ‘yan Ƙalilan da suka yi hannun riga da miyagun halayen nan da aka san ‘yan siyasa da su wato Ƙarya, cin amana da rashin cika alƘawari. A cikin irin waɗannan ‘yan siyasa da ba su wuce a kirga ba a faɗin Jahar Katsina shi ne shugaban majalisar dokoki mai ci yanzu, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-Gwajo, saboda gaskiya da riƘon amana tare da kishin al’ummarsa tun farkon wannan mulki na dimokuraɗiyya, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-Gwajo yake riƘe da muƘamin siyasa wanda jama’a ne suka zaɓe shi ba naɗa shi aka yi ba.

A shekarar 1999 ne al’ummar Ƙaramar hukumar Mai’Aduwa suka zaɓi Alhaji Ya’u Umar Gwajo-Gwajo a matsayin shugaba saboda a ƘarƘashin tutar jam’iyyar PDP bisa la’akari da halayensa na Ƙwarai da mu’amalarsa da jama’a. Babu shakka mutanen Mai’Aduwa ba su daga cikin mutanen wasu Ƙananan hukumomi da ke cizon yatsa domin Allah ya yi masu gyaɗar dogo ba, su yi zaɓen tumun dare ba, domin Gwajo-Gwajo bai bai wa mutanensa kunya ba, ta hanyar jajircewa wajen gudanar masu da ayyukan ci gaban rayuwarsu. Irin ayyukan da Gwajo-Gwajo ya yi waɗanda sun fi a Ƙirga sun haɗa da inganta aikin noman rani wanda shi ne muhimmiyar sana’ar da mutanen Mai’Aduwa suka dogara a kanta. Ya giggina hanyoyi, makarantu, asibitoci, rijiyoyin burtsatse da haɗa garuruwa da dama da hasken wutar lantarki. Saboda irin ci gaban da Ƙaramar hukumar Mai’Aduwa ta samu a lokacin mulkin Gwajo-Gwajo shi ne ya sa tarihin wannan Ƙaramar hukuma ba zai taɓa kammatuwa ba, ba tare da ambato sunan Gwajo-Gwajo ba.

Saboda irin yadda ya tafiyar da mulkinsa bisa gaskiya tare da riƘon amana ya sa Gwajo-Gwajo ya shahara tare da tsere wa tsara yaƘin masarautar Daura duk da cewar, yankin ne jagoran jam’iyyar adawa kuma ɗan takarar jam’iyyar CPC wato Janar Muhammadu Buhari ya fito. A shekarar 2003 bayan da Janar Buhari ya tsunduma cikin harkokin siyasa har ya zamo ɗan takarar shugaban Ƙasa na jam’iyyar ANPP ya tato guguwar canji ba a mahaifarsa kawai ba, a duk faɗin Jahar Katsina. A zaɓen wannan shekarar duk da cewar, Janar Buhari bai kai labari ba amma ya yi sanadiyyar gagarumar asara ga jam’iyyar PDP domin ta yi asarar kujerunta tun daga majalisar jaha har zuwa ta dattawa.

Shi kansa jagoran tafiyar wato marigayi tsohon shugaban Ƙasa, Umaru Musa ‘Yar’Aduwa da Ƙyar ya tsira. Amma duk da wannan guguwar sauyi sai da Gwajo-Gwajo ya kawo wa jam’iyyar PDP Ƙaramar hukuma, Mai’Aduwa. Ita takance zakka ga ANPP a masarautar Daura a wancan lokacin domin duk ta lashe su. Wannan ƘoƘari na Gwajo-Gwajo shi ya Ƙara fitar da sunan shi a kowane lungu da saƘo na Jahar Katsina. Don haka ne a wannan lokacin tsohon shugaban Ƙasa, Malam Umaru ‘Yar’Aduwa ya sakankance tare da jawo Gwajo-Gwajo a jikinsa don ya tabbata gwarzo abokin tafiya. A wannan lokaci Gwajo-Gwajo ya zama kwamandan rundunar yaƘi na Umaru Musa ‘Yar’Aduwa da kuma jam’iyyarsa ta PDP a yankin masarautar Daura, domin duk abin da ya sa gaba, to, da Ƙarfin Allah sai ya sami nasara. Bisa ga irin alherin da Gwajo-Gwajo ya jawo wa masarautar Daura ne, ya sa marigayi Mai Daura, Mamman Bashar ya ga cewa, babu wani mahaluki da ya dace da sarautar Garkuwan Daura illa Alhaji Ya’u Umar Gwajo-Gwajo. Ayyukan alheri da taimakon jama’a na Gwajo-Gwajo ba a masarautar Daura ko Jahar Katsina suka tsaya ba domin har zarce maƘwabtan Ƙasashe don haka ne Mai Martaba Sarkin Sultan na Damagaram ya naɗa shi a matsayin Turakin Damagaram.

Kazalika da aka zo zaɓen Ƙananan hukumomi a karo na biyu ba tare da kai ruwa rana ba, Gwajo-Gwajo ya sake ɗarewa shugaban Ƙaramar hukuma ba tare da wata hamayya ba.

Bayan ya kammala mulkinsa a wa’adi na biyu mutanen Ƙaramar hukumarsa sun sake amince masa da ya wakilce su a majalisar dokoki ta jaha a shekarar 2007. A wannan karo ma an yi gumurzu domin kuwa jam’iyyar ANPP ta sake tsayar da Janar Buhari takarar shugaban Ƙasa, amma duk da haka sai da Gwajo-Gwajo ya yi kaye. Duk kuwa da cewar, guguwar canji ta Janar Buhari ta cinye kujerun PDP da dama musamman a yankinsu na masarautar Daura, wato mahaifar Janar Buhari.

Bayan da aka zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar dokokin Jahar Katsina, mutane da dama sun yi hasashen cewa, yana da wahala a ce ‘yan majalisar ba su amince wa Gwajo-Gwajo zamo wa shugabansu ba, domin kuwa Hausawa na cewa, “Ice mai kama ka Ƙota”. Wannan hasashe da jama’a suka yi kuwa ya yi daidai da ra’ayin ‘yan majalisar domin kuwa a zamansu na farko suka amince masa ya zama shugabansu. Duk da cewar, shugabancin majalisa na cike da Ƙalubale iri-iri, Gwajo-Gwajo ya ciri tuta ta hanyar gudanar da majalisar da ba a taɓa yin irinta ba a tarihin Jahar Katsina musamman wajen aiwatar da dokoki da Ƙudurorin da suka kawo ci gaban al’umma. Saboda ɗaukar girma, rashin girman kai tare rashin handama da babakere ya sanya kowane ɗan majalisa ke jinjina masa tare da ba shi girma. Saɓanin majalisun wasu jahohi da kan zama tamkar fagen dambe saboda rigingimu, majalisar Jahar Katsina sun zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya duk da cewar, akwai ‘yan jam’iyyar adawa ba kuwa saboda komai ba illa saboda kamanta adalci irin na Gwajo-Gwajo.

Waɗanda ba su fahimci aikin majalisa ba kan tsargi ‘yan majalisa da cewa, sun zama ‘yan amshin shatar gwamnoni wanda abin ba haka yake ba, domin idan har majalisa ba ta bai wa Gwamna haɗin kan da ya kamata ba, to, da wahala ya iya aiwatar da ayyuka na a-zo-a-gani. MatuƘar ana faɗa tsakanin majalisa da ɓangaren zartarwa, to, babu wanda zai yi asara sai talakawa. Saboda irin goyon baya da haɗin kai da majalisar dokokin Jahar Katsina ke bai wa ɓangaren zartawa ƘarƘashin jagorancin, Alhaji Ibrahim Shehu Shema ne yasa a tsawon shekaru biyar da suka gabata Shema ya sami nasarar gudanar da ayyukan ci gaban da ya zarce na kowane Gwamna a Ƙasar nan. A maganar da ake yanzu yana da wahala a sami wata jaha a Najeriya da za ta iya gogayya da Jahar Katsina a fannonin ci gaban al’umma daban-daban irin su hanyoyin mota, wutar lantarki, ruwan sha, gidaje, asibitoci da sauransu.

A dangantakar shi da jama’a kuwa, Gwajo-Gwajo ya zama dole a jinjina masa bisa yadda yake ƘoƘarin sauraren jama’a ba wai na mazaɓarsa kawai, a’a, daga duk inda mutum ya fito a faɗin Jahar Katsina. A gidansa ko a ofishinsa bai taɓa gajiyawa ba da sauraren jama’a tare da tallafa masu gwargwadon iyawarsa ba tare da la’akari da inda mutum ya fito ba.

Irin wannan ƘoƘari da Gwajo-Gwajo ya daɗe yana yi shi ne ya sanya a zaɓen da ya gabata ma ba ta canza ba duk da cewar, Janar Buhari ya ƘirƘiro sabuwar jam’iyya wato CPC kuma ta tsayar da shi takarar shugabancin Ƙasa wanda wannan ya turo wata sabuwar guguwar canji. Wannan guguwar canji za a ce ta fi ta baya Ƙarfi. Domin baicin taimako na Allah da PDP ta samu, da an yi mata wa ka ci ka tashi. Duk da cewar, PDP ta tafka mummunar asarar kujeru uku na majalisar dattawa da kujeru sha biyu majalisar wakilai amma ta sami galaba ta hanyar lashe zaɓen Gwamna da kuma kujeri masu rinjaye na majalisar dokoki wanda Gwajo-Gwajo na daga cikin ‘yan majalisar da suka tsira da kujerarsu.

Wannan ne ya ba shi dama ya sake hayewa bisa kujerarsa ta shugabancin majalisar dokoki na Jahar Katsina a karo na biyu, inda ya kafa wani sabon tarihi kasancewarsa mutum na farko da ya riƘe wannan muƘami har sau biyu. Wannan karo ma mai girma shugaban majalisar dokokin na Jahar Katsina bai yi Ƙasa a gwiwa ba wajen daidaita sahun wannan majalisa don tabbatar da ganin cewa, gwamnatin Alhaji Ibrahim Shehu Shema ta ci gaba da yi wa jama’a ayyukan alherin da ta saba. A wannan zango ma, majalisar dokokin ta Jahar Katsina ta sake ɗinkewa domin fuskantar duk wani Ƙalubale. Bisa la’akari da yadda Gwajo-Gwajo ya riƘe amanar da mutanensa suka ɗora masa za mu iya cewa, ‘yan siyasa suna kawai suka tara domin tabbas akwai mutanen Ƙwarai masu fitar da kitse daga wuta. Kuma da ma Hausawa sun ce “A daɗe ana yi sai gaskiya”.

DIKKO BALA Ƙ/SAURI, Ya Ruwaito Ne Daga Ƙofar-Sauri, Katsina. 08036972442.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.