Hakimin Bununu Ya Yaba Wa Gwamnatin Bauci Sababbin Masarautu

0
1052

Umar Saye, Daga Bauci

SABON Hakimin Ƙasar Bununu da ke Ƙaramar hukumar Tafawa Ɓalewa, Alhaji Salisu Mohammed ya yaba wa gwamnatin Jahar Bauci da masarautar Bauci saboda ƘirƘiro sababbin masarautun hakimai da aka yi a Jahar Bauci tare kuma da inganta darajar sarakunan gargajiya a jahar.

Sabon Sarkin ya bayyana haka ne a wajen bikin naɗin sarautarsa wanda ya gudana a fadar Mai Martaba Sarkin Bauci da kuma fadarsa da ke garin Bununu, inda ya bayyana cewa, naɗa sababbin hakiman wata dama ce ta karrama gidajen sarauta da kuma kusantar da talakawa ga shugabanninsu.

Don haka ya bayyana cewa, a shirye yake wajen ganin ya samar da shugabanci mai amfani ga jama’arsa da masarautar Bauci, don haka ya ja hankalin al’ummarsa da su kasance masu yi wa shugabanni biyayya da kuma dogaro da kansu wajen karatu da kasuwanci da noma kamar yadda Shehu Usman Ɗanfodiyo ya yi umarni.

Alhaji Salisu Mohammed ya bayyana aniyarsa ta haɗa kai da gwamnati wajen ciyar da yankin gaba da kuma tashi tsaye don kare muradun mutanen Ƙasar Bununu da kewaye. Don haka ya buƘaci kowane mutum a yankin ya Ƙaunaci ɗan uwansa a zauna lafiya da juna shi ne zai samar da ci gaba mai amfani.

Shi ma a nasa jawabin Mai Martaba Sarkin Bauci, Alhaji Rilwanu Sulaimanu Adamu ya ja kunnen sababbin hakimai bakwai da ya naɗa a Ƙaramar hukumar Tafawa Ɓalewa, su kai rahoton waɗanda ba su amince da su ba ga hukuma, kuma ya bayyana cewa, ba zai saurari duk wani masaraucin da ya kai talakansa kotu kan rikicin fili ba matuƘar za a iya sasanta rigimar a masarautarsa, don haka ya ja kunnensu kan su daina haɗa kai da ma’aikatan gwamnati wajen sayar da filaye da gonakin jama’a kuma su nisanci raba gado saboda haƘƘi ne na shari’a ya kamata su kai wa mahukunta don gudun abin da zai je ya dawo.

Hakimai bakwai da aka naɗa, sun haɗa da Alhaji Adamu Abdullahi Hakimin Kardan da Alhaji Salisu Mohammed Hakimin Bununu da Malam Isa Dauda Hakimin Ball da Alhaji Abdullahi Hassan Hakimin Dull da Alhaji Abdulrashid Adamu Mu’azu Hakimin Boto da Alhaji Abdullahi Yakubu Hakimin Boi da Alhaji Aliyu Abubakar Hakimin Lere.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.