’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 4 A Song

0
521

MUHAMMAD SHAFI’U SALEH, Daga Yola

WASU ‘yanbindiga sun kai hari a garin Song kimanin kilomita 100 daga Yola fadar jahar harin da ya yi sanadiyyarmutuwar mutum huɗu tare da Ƙone sakatariyar Ƙaramar hukumar da Ƙone ofishin rundunar ‘yan sanda da ke Song cikin Jahar Adamawa.

Wannan harin dai shi ne karo na uku da ‘yan bindiga ke kaiwa a jahar cikin Ƙasa da mako ɗaya wanda kuma ‘yan bindigar sun kai harin a makon jiya, inda kuma wata yarinya ‘yar kimanin shekara 10 ta gamu da ajalinta a yayin harin.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jahar Adamawa, DSP Ibrahim Muhammad ya tabbatar da faruwar harin da ‘yan bindigar suka kai garin Song inda kuma ya yi Ƙarin bayani da cewa, cikin dare ne wasu mahara suka kai hari da manyan bindigogi suka kai hari a ofishin ‘yan sanda da kuma sakatariyar Ƙaramar hukumar Song inda kuma ya ce sun kashe mutum huɗu.

Ya ce cikin mutum huɗu da ‘yan bindigar suka kashe har da jami’in soja ɗaya da kuma jami’in ɗan sanda da wata mata ‘yar shekara 80 da kuma wata yarinya jikarta wacce ita ma harin ya rutsa da ita kana ya tabbatar da cewa, kawo lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ba ta kama kowa ba.

DSP Ibrahim Muhammad ya kuma bayyana cewa, a yayin harin wasu motoci sun Ƙone Ƙurmus a sakatariyar Ƙaramar hukumar ta Song kana ya kuma yi kira ga jama’ar jahar da su taimaka masu da bayanai ta yadda za su kai ga cafke ɓata-garin da ke kai irin waɗannan hare-hare a duk faɗin Jahar Adamawa.

Tuni dai mataimakin sufeto-janar na rundunar ‘yan sanda shiyya ta uku da ke Yola, AIG Tambari Yabo Muhammad da kwamishinan ‘yan sanda na jahar, Mista Gopherel Emeka Okeke suka kai ziyarar gani da ido a yankin da aka kai harin da ke Ƙaramar hukumar ta Song.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.