An Tsinci Gawar Wani Jariri A Leda A Rigasa

0
1901

USMAN NASIDI DAGA KADUNA

A ranar litinin  da ta  gabata ne da safe wasu al’ummar da ke zaune a titin Makarfi da ke  sabon garin Rigasa Kaduna suka tsinci gawar wani jariri da mahaifarsa a cikin wata bakar leda da aka jefa shi a cikin ruwan rafin da ke karkashin gadar titin shiga unguwar.

Wakilinmu daya ziyarci wurin da lamarin ya auku, ya gano cewa shi wannan jaririn sabon haihuwa ne kuma mai cikakken halitta, dukda ba a san wanda ya ajiye shi ba kafin wasu bayin Allah sun ciro shi a sanya shi a cikin kwali.

Wani daga cikin mutanen da suka sanya aka ciro shi Malam Abdullahi Mai Faci (Ya Baba), ya bayyana cewa wasu kananan yara ne dake wasa a bakin rafin ne suka ganshi kuma sanar dashi inda ya sanya wasu yaran ciro shi daga cikin ruwan.

Acewarsa, bayan fito da yaron ne suka cire shi a ledar da yake ciki sannan suka sanya shi a cikin wani kwali kafin ya aika kiran mai unguwar dake yankin, don sanin mataki na gaggawa da za a dauka kafin a birne shi.

Ya baba Mai Faci, ya kara da cewa ganin wannan lamarin ne yasa suka kira ‘yan jaridu da ‘yan sanda don daukar matakin na gaggawa da kara yin kira da jan hankalin ga jama’a akan su kara tsoron Allah a zukatansu.

Hakazalika, wata matar dake zaune a kusa da wurin da lamarin ya auku Malama Maryam, ta bayyana cewa wannan shi ne karo na uku (3) da suka ga lamarin ya auku bayan dawowar su nan unguwar,

Ta kara da danganta laifin da sakaci na iyaye mata don ba ta yadda za ayi yarinya tayi ciki iyayenta mata ba su gane ba, ko su ke gallazawa yaran bayan sun yi cikin, har su sanya su jefar da jaririen bayan sun haihu.

Mai Unguwar yankin titin Makarfin Malam Mohammad Jibrin, ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma bayyana cewa daga gani jaririn kawo shi akayi aka jefa daga wani waje amma ba yaran unguwar ne suka aikata hakan ba.

A karshe, Malam Jibrin, ya yi Allah wai da wannan dabi’ar, kuma ya yi kira ga iyayen yara mata da su kara kulawa ta hanayar  sa ido ga yaransu, sun kuma binne gawar yaron bayan zuwan yan sanda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.