Ya Dace Gwamnatin Saudiyya Ta Rika lura Da Masu Aikin Hajji A Kasarta – Sheikh Jingir

0
1235

Shugaban majalisar malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa. Kuma Amirul hajji na  jihar Filato a aikin hajjin da aka gudanar a bana, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir.,a  tattaunawar  da ya yi da wakilinmu Isah Ahmad Jos  ya bukaci gwamnatin Saudiya  ta kara sanya ido, ga irin mutanen da suke shigar kasar don aikin hajji, don ganin an magance sake faruwar hadurran  da suka faru lokacin  aikin hajjin da ya gabata. a kuma bayyana irin nasarorin da aka samu a aikin Hajjin bana ga dai yadda Tattaunawar ta kasance ayi karatu lafiya.

GTK; Mene ne Malam zai ce dangane da haxarin da ya faru a wajen jifa
da kuma haxarin da ya faru lokacin da wani gugar karfe ya faxowa
alhazai a Makka lokacin aikin hajji?

Sheikh Jingir; To, ni ban tava yin aikin hajjin da ya xaga mani
hankali ba, kamar wannan  aikin hajji na bana ba.  Saboda wannan
waqi’a guda biyu da suka faru waxanda  suka  tafi da rayukan alhazan
duniya wasu  kuma suka sami raunika. Muna rokon Allah ya gafartwa
waxanda suka rasa rayukansu a waxannan haxarurruka kuma muna rokon
Allah ya baiwa waxanda suka sami raunuka lafiya.

Kuma ina kira ga musulmin duniya kan kada su  yarda da farfagandar da
‘yan shi’a da kuma qasar Irin  suke yi, kan wannan al’amari  na
cusawa musulmin duniya  rashin yarda da qaddara kan wannan  haxarin da
ya faru. Babu wanda zai mutu sai lokacinsa ya qare, kuma babu wanda
zai mutu a wannan sanadi sai wanda Allah ya rubuta sunansa.
Kuma  ina kira ga  gwamnatin Saudiya da gwamnatin Nijeriya su binciki
waxannan  haxarurruka  da ya faru a lokacin aikin haji. Kuma suyi
hankali da abokan gaba.

Ganin irin abubuwan da suke faruwa a duniya  ya kamata gwamnatin
Saudiya ta  qara zuba ido ga mutanen da suke zuwa aikin hajji.
Gwamnatin Saudiya ta zuba ido sosai domin yanzu duniya ta canza, tun
da a yanzu za a kaiwa musulmi hari a masallaci da kasuwa da gona da
tashoshin mota da sauran wurare.  Idan masu irin wannan hali suka sami
dama ko a lokacin aikin hajji ma zasu iya kai  hari.

GTK; To, mene ne Malam zai ce kan shawarar da wasu suke bayarwa kan
faruwar waxannan haxarurruka  cewa ya kamata a shigar da wasu qasashen
musulmi a cikin  shirya aikin hajjin da Saudiya take yi?

Sheikh Jingir; Masu wannan magana na cewa wasu qasashe su qarvi shirya
aikin hajji daga qasar Saudiya.  Tambayar da zan yi masu ita ce a Iran
Ka’aba take ko a Makka? shin ya dace kowace qasa idan ta sami man
fetur nata?  amma ace za a kwacewa mutanen Makka aikin hajji, wanda
nasu ne ? Kai taka qasar taka, amma su mutanen Makka qasarsu bata su
bace? wannan xanyen hukumci ya yi daidai?

Kuma a duk duniya  wace qasa ce take sauke baqi kamar Saudiya?  ta
basu abinci ta basu  ruwa, saboda haka wannan magana bata da tushe.

GTK; Waxanne irin nasarori ne kake ganin cewa an samu  a aikin hajjin
bana musamman a bangaren hukumar alhazai ta qasa da kuma su qasar
Saudiya?

Sheikh Jingir; Wato tun daga shekara ta 1977  da na fara tafiya aikin
hajji zuwa wannan shekara, ban tava ganin irin cigaban da na gani
kamar  a aikin hajjin bana ba, daga alhazan Nijeriya.

A aikin hajjin bana naga ikon Allah kan baiwa alhazanmu abinci. Jihohi
da dama sun baiwa alhazansu abinci.Bayan haka naga yadda  aka kai
likitoci suka riqa duba alhazai a lokacin aikin hajjin bana.

Saboda haka na yabawa Amirul hajji na qasa mai martaba Sarkin Kano
Alhaji Sunusi Lamixo Sunusi kan wannan nasara da aka samu.

Haka kuma ina yabawa qasar Saudiya domin duk duniya a tawa fahimtar,
kamar yadda na faxa a baya, babu qasar da take saukar baqi a duk
shekara  masu yawa kamar Saudiya.  A lokacin umara da lokacin aikin
hajji tare da bayar da abinci da ruwa da likitoci da magunguna kyauta.

GTK; To,  matsayinka na Amirul hajji  jihar Filato a bana, waxanne
irin nasarori ne kuke ganin kun samu a aikin hajjin bana?

Sheikh Jingir; Babu shakka mun sami nasarori masu tarin yawa a aikin
hajjin bana, domin dukkan alhazan da suka biya  kuxin kujera a hukumar
alhazai ta jihar Filato a bana, babu wanda bai sami tafiya ba.
Savanin abubuwan da suka riqa faruwa a shekarun baya, a inda mutane
zasu biya kuxin kujera, amma daga qarshe su kasa samun tafiya aikin
hajji.

Bayan haka dukkan alhazanmu na jihar Filato mun tafi Saudiya a kan
lokaci kuma mun wuce zuwa Madina gabaki xaya, muka je muka gudanar da
ziyarce ziyarce daga nan muka wuce zuwa Makka.

Haka  kuma  wata babbar nasara da muka samu a bana, ita ce an rabawa
alhazan jihar Filato abinci a lokacin aikin hajji kyauta. Domin a
lokacin da aka naxa ni amirun hajji na jihar Filato, na tarar da
gwamnan jihar  Barista Simon Lalong na bashi  shawara a riqa baiwa
alhazan jihar Filato abinci a lokacin aikin hajji, kuma nan take ya ce
ya qarvi wannan shawara. Don haka a bana an baiwa alhazan Filato
abinci da suka haxa da shinkafa da kaji da shayi da kwai da safe da
rana da daddare.

Bayan haka a haxarurrukan nan guda biyu da suka faru a lokacin aikin
hajji babu wani alhajin Filato da ya rasa ransa.

A dukkan alhazanmu na jihar Filato  mutum biyu ne suka rasa rayukansu
a lokacin aikin hajji. Alhazan da suka rasu sune akwai  xaya daga
jihar Taraba wanda yazo ya biya a jihar Filato, akwai  kuma wani  daga
jihar Bauchi wanda shima  yazo ya biya a nan jihar Filato.

Sai da dukkan alhazamu suka gama tasowa zuwa gida  sannan ni da
shugaban kwamitin aikin hajji na jihar Filato Alhaji Xanlami Muhammad
da sauran tawagarmu  muka taso muka dawo gida. A takaice  mun je mun
yi aiki lafiya kuma  mun dawo lafiya.

GTK; Meye Malam zai ce kan yadda wasu jami’an alhazai a jihohi suke
cinye kuxaxensu a  qasar nan?

Sheikh Jingir; Wannan matsala da take faruwa wani babban abin takaici
ne, don haka lallai ya zama wajibi gwamnatocin jihohi da gwamnatin
tarayya su duba wannan matsala ta cinyewa alhazai kuxaxe dake faruwa a
duk shekara.  Abin da takaici ace mutum ya yi nomansa ko kuma ya yi
kiwonsa ya sayar ya kawo kuxi ya biya don ya tafi aikin hajji, amma a
sami wasu su cinye. Wannan abu yana faruwa  a jihohi da dama a qasar
nan. Wallahi wani saboda shiga rai irin na aikin hajji, idan aka cinye
masa kuxin aikin  hajji da ya biya,  sai ya haxiyi zuciya. Don haka
lallai a tashi a magance wannan matsala.

Kuma ina son nayi amfani da wannan dama wajen yin kira ga gwamnatin
tarayya da gwamnatocin jihohi, kan idan za a bada aikin jagorancin
alhazai to a riqa baiwa malaman addinin musulunci. Idan aka  yi haka
za a magance dukkan irin waxannan matsaloli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.