Ya Dace Manoma Su Kusanci Gwamnati – Maigari Daniel

0
742

RABO HALADU DAGA KADUNA.

An shawarci kananan manoma da ke fadin jihar kaduna, dasu mike wajen shiga
kungiyoyin manoma domin samun kusancin daya dace daga wajen gwamnati.
Kwamishinan ma’aikatar ayyukan gona ta jihar kaduna, Mista Manzo Daniel
Maigari ya bada wannan shawara a yayin wani taron manema labarai daya
gudana a sakatariyar ‘yan jaridu ta kasa da ke  kaduna.
Mista Maigari,  ya ci gaba da cewar shiga kungiyoyin manoma wata hanyace mai
sauki wacce za ta sadar da manoma da gwamnati har a kai ga samun biyan
bukata.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa  a duk shekara kananan manoma a jihar kaduna suna
samar da dimbim masara da sauran kayan  amfanin gona, wanda ake neman saye
ruwa a jallo a ciki da wajen jihar, amma rashin kasancewarsu a kungiyance
yana mayar da hannun agogo baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.