Ban Amince Ba Cewa Wai Yan Jarida na Mutuwa Da Talauci- Nazifi Muryar Unity

0
2106

Nazifi Abdullahi wanda ake yi wa lakabi da Muryar Unity, dan jarida ne da ya yi fice  a gidan rediyon Unity FM Jos. Ta hanyar shirye shiryen da yake gabatarwa a wannan gidan rediyo da suka hada da Dandalin maza da tsarabar masoya da tauraron makada da dai sauransu.

A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu Isah Ahmad Jos, ya bayyana cewa shi  har yanzu bai amince ba    cewa ‘yan jarida suna mutuwa a talauce, Domin shi a wajen sa  aikin jarida ya yi masa komai na arziqi,ga dai yadda tattaunawar ta kasance ayi karatu lafiya.

GTK: Da farko zamu so muji tarihin rayuwarka

Nazifi Abdullahi; To, ni dai  sunana Nazifi Abdullahi, an haifeni ne a wannan gari na Jos. Na yi makarantar firamare da makarantar sakandire na duk  a nan garin Jos. Daga nan  kuma nayi jami’a  inda na karanci harkokin  aikin jarida. Nayi aiki da gidan Ray Power da ke nan garin Jos, A yanzu kuma gashi ina aiki a gidan rediyon Unity FM da ke  garin Jos.

GTK: Meye ya karfafa maka gwiwar shiga wannan aiki na rediyo?

Nazifi Abdullahi; Wato ni tun ina karami idan naga ana labarai ko kuma idan naga mutum yana magana a rediyo, sai naji ina ma nine. Wannan dalili yasa na lashi takobin in Allah ya yarda, wata rana nima  sai an nunani a TV ko kuma nayi magana a rediyo.

Bayan na girma sai naji bana son Talbijin, sai naga yafi dace mini nayi aikin rediyo maimakon aikin gidan Talbijin. A lokacin  da aka gayyaceni nazo na kama aiki a wannan gidan rediyo na Unity FM Jos  sai na kara kaunar
aikin jarida. Wanda ko  mutuwa na yi, idan na  dawo duniya to aikin rediyo zan yi. Saboda kaunar da nake yiwa aikin. Wannan shi ne ya karfafa mani gwiwar shiga wannan aiki .

GTK: Maye ya sanya kace ko zaka mutu ka dawo aikin rediyo zaka yi?

Nazifi Abdullahi, Saboda a duk lokacin da na rike abin magana ma’ana idan na hau kan kujerar aiki, babu abin da nake ji sai nishadi  Koda bakin ciki nake ji idan har nazo na hau kan kujerar aiki, sai naji na manta da wannan bakin ciki farin ciki ya lullubeni, saboda wannnan aiki yana sani farin ciki.

GTK: A wane lokaci ne ka fara wannan aiki?

Nazifi Abdullahi: Na shiga aikin rediyo ne tun kamar shekaru 15 da suka gabata, na fara aiki da tashar rediyon  Ray Power  daga nan na dawo wannan gidan rediya na Unity. Nayi shekaru kamar 10 ina aiki a gidan rediyon Ray Power. Daga nan da Allah yasa tsohon ministan sadarwa Alhaji Ibrahim Dasuki Salihu Nakande  ya bude wannan gidan rediyo na Unity, sai na dawo nan aiki.

GTK: Kamar wadanne shirye shirye ne kake gabatarwa a wannan gidan rediyo na Unity FM?

Nazifi Abdullahi: Shirye shiryen da nake gabatarwa a wannan gidan rediyo na Unity FM Jos  su ne  dandalin maza wanda yake magana kan zamantakewar mazaje da iyalansu  da tsarabar masoya da tauraron makada da dai sauransu.

GTK: Daga lokacin da ka fara wannan aiki zuwa yanzu kamar wadanne irin kalubale ka fuskanta?

Nazifi Abdullahi: To, kamar yadda ka sani ne shi aikin jarida dama ya kunshi kalubale mai tarin yawa. Hakika a lokacin da nake aiki a gidan rediyon Ray Power  Kalubalen da na fuskanta a wannan gidan rediyo, yasa naji kamar in bar aiki a gidan rediyon a lokacin.

kamar a wurin aiki akwai matsaloli irin na aiki, wani lokaci zaka ji wani ya yaba maka wani lokaci kuma kaji wani ya kushe maka. Bayan haka akwai wani kalubale wanda kana cikin gabatar da wani shiri sai a canza maka shi, musamman bana mantawa akwai wani shiri da nake yi a wannan gidan rediyo mai suna duniyar fina finai, a  lokacin da aka raba ni da wannan shiri   sai da nayi kwalla. Ita manajan wannan gidan rediyo Hajiya Larai Baba, ta ce na yi hakuri dama aikin jarida ya gaji haka. To, amma da taimakon Allah irin wadannan kalubale da zarar ya taso sai yazo ya wuce.

GTK: Wadanne irin nasarori ne kake ganin ka cimma a wannan aiki?

Nazifi Abdullahi, Ai nasarorin da na samu a wannan aiki suna nan da dama, Don nasarori kamar na bangaren jama’a na sami nasara ta dalilin wannan aiki,   shi yasa ake yi mani lakabi da muryar Unity. Kamar yadda na fada maka,kafin na fara wannan aiki babu wanda ya sanni.

Amma a yanzu sakamakon wannan aiki  duk inda na shiga sai naga mutane sun sanni. Bayan haka wata nasarar kuma ita ce wannan aiki ya koyar dani tsoran Allah ya kuma koyar da ni girmama na gaba  da mutumta na
baya.

Sannan kuma nasara ta bangaren dukiya ko kudi sai dai nace na gode Allah. Don ina mai tabbatar maka kamar abin da ya shafi abinci da abin sha, idan kaje gidana sai ka ture. Kuma duk ba da kudina nake saye ba. Haka kawai sai mutum ya kirani saboda wannan aiki da nake yi, ya ce ga kudi nan ya saka mani a asusun ajiyata na banki. Ko a ‘yan kwanakin nan akwai wasu makudan kudi da wani mutum ya bani, da na karba sai da na dada jinjinasu naji dadi kuma a zuciyata nace lallai wannan aiki ne wanda mutum zai kara rike shi hannu bibiyu.

Bayan haka na sami kyaututtukan karramawa da dama  daga kungiyoyi daban daban  a wannan garin  Jos.

Wasu suna cewa aikin jarida ba aiki ne da ake samun kudi ba, ko kuma ‘yan jarida suna mutuwa a talauce ba, ni ban amince  da wannan ba. Domin kamar yadda ka gani yanzu ta dalilin wannan aiki ina da gida da fili nawa na kaina. Ina da duk wani abu na rayuwa ta dalilin wannan aikin jarida. Saboda haka ni babu abin da zance a kan wannan aiki sai dai nace na gode Allah.

GTK; Mene ne sakonka ga al’umma musamman matasa masu sha’awar wannan aiki?

Nazifi Abdullahi; Sakona ga al’umma musamman masu sha’awar wannan aiki na jarida shi ne duk wanda ya sami kansa a wannan aiki, ya rika  hakuri da gaskiya. Kuma ya zamanto mai jajircewa mai tausayin na baya tare da
girmama na gaba. Idan har mutum ya rike wadannan  abubuwa zai sami nasara. Don aikin jarida baki daya  aiki ne na gyaran   tarbiya, idan babu girmama mutane, ba zaka taba zuwa ko’ina ba, idan baka da godiyar Allah ba zaka taba zuwa ko’ina ba. Don haka sakona ga matasa masu sha’awar wannan aiki shi ne su rike gaskiya su girmama na gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.