Ban Yarda ‘Yan Jarida Suna Mutuwa A Talauce Ba–NAZIFI Muryar Unity

0
3176

Isah Ahmed Daga  Jos

NAZIFI Abdullahi wanda ake yiwa lakabi da Muryar Unity, dan jarida ne
da ya yi fice  a gidan rediyon Unity FM Jos. Ta hanyar shirye shiryen
da yake gabatarwa a wannan gidan rediyo da suka hada da Dandalin maza
da tsarabar masoya da tauraron makada da dai sauransu.

A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana cewa shi  bai
yarda da maganar da wasu suke yi ba,  cewa ‘yan jarida suna mutuwa a
talauce. Domin shi a wajen sa  aikin jarida ya yi masa komai na
arziki.

Ga dai yadda tattaunawar ta kasance

GTK; Da farko zamu so muji tarihin rayuwarka

NAZIFI Abdullahi; To, ni dai  sunana NAZIFI Abdullahi, an haifeni ne a
wannan gari na Jos. Nayi makarantar firamare da makarantar sakandire
duk  a nan garin Jos. Daga nan  kuma nayi jami’a  inda na karanci
harkokin  aikin jarida. Nayi aiki da gidan Ray Power dake nan garin
Jos. A yanzu kuma gashi ina aiki a gidan rediyon Unity FM dake nan
garin Jos.

GTK; Meye ya karfafa maka gwiwar shiga wannan aiki na rediyo?

NAZIFI Abdullahi; Wato ni tun ina karami idan naga ana labarai ko kuma
idan naga mutum yana magana a rediyo, sai naji ina ma nine. Wannan
dalili yasa na lashi takwabin in Allah ya yarda, wata rana nima  sai
an nunani a TV ko kuma nayi magana a rediyo.

Bayan na girma sai naji bana son TV, sai naga yafi dace mani nayi
aikin rediyo maimakon aikin gidan TV. A lokacin  da aka gayyaceni nazo
na kama aiki a wannan gidan rediyo na Unity FM Jos  sai na kara kaunar
aikin jarida. Wanda a yau koda mutuwa zan yi, idan na  dawo duniya to
aikin rediyo zan yi. Saboda kaunar da nake yiwa aikin. Wannan shi ne
ya karfafa mani gwiwar shiga wannan aiki .

GTK; Maye ya sanya kace ko zaka mutu ka dawo aikin rediyo zaka yi?

NAZIFI Abdullahi; Saboda a duk lokacin da na rike abin magana ma’ana
idan na hau kan kujerar aiki, babu abin da nake ji sai nishadi. Koda
bakin ciki nake ji idan har nazo na hau kan kujerar aiki, sai naji na
manta da wannan bakin ciki farin ciki ya lulluveni. Saboda wannnan
aiki yana sani farin ciki.

GTK; A wannan lokaci ne ka fara wannan aiki?

NAZIFI Abdullahi; Na shiga aikin rediyo ne tun kamar shekaru 15 da
suka gabata. Na fara aiki da tashar rediyo ta Ray Power  daga nan na
dawo wannan gidan rediya na Unity.

Nayi shekaru kamar 10 ina aiki a gidan rediyon Ray Power. Daga nan da
Allah yasa tsohon ministan sadarwa Alhaji Ibrahim Dasuki Salihu
NaKande  ya bude wannan gidan rediyo na Unity, sai na dawo wajen.

GTK; Kamar wadanne shirye shirye ne kake gabatarwa a wannan gidan
rediyo na Unity FM?

NAZIFI Abdullahi; Shirye shiryen da nake gabatarwa a wannan gidan
rediyo na Unity FM Jos  su ne  dandalin maza wanda yake magana kan
zamantakewar mazaje da iyalansu  da tsarabar masoya da tauraron makada
da dai sauransu.

GTK; Daga lokacin da ka fara wannan aiki zuwa yanzu kamar wadanne irin
kalubale ka fuskanta?

NAZIFI Abdullahi; To, kamar yadda ka sani ne shi aikin jarida dama ya
kunshi kalubale mai tarin yawa. Hakika a lokacin da nake aiki a gidan
rediyon Ray Power  Kalubalen da na fuskanta a wannan gidan rediyo,
yasa naji kamar in bar aiki a gidan rediyon a lokacin.

kamar a wurin aiki akwai matsaloli irin na aiki. Wani lokaci zaka ji
wani ya yaba maka wani lokaci kuma kaji wani ya kushe maka. Bayan haka
akwai wani kalubale wanda kana cikin gabatar da wani shiri sai a canza
maka shi. Musamman bana mantawa akwai wani shiri da nake yi a wannan
gidan rediyo mai suna duniyar fina finai. A lokacin da aka raba ni da
wannan shiri ina ganin sai da nayi kwalla. Ita manajan wannan gidan
rediyo Hajiya Larai Baba ta ce nayi hakuri dama aikin jarida ya gaji
haka. To, amma da taimakon Allah irin wadannan kalubale da zarar ya
taso sai yazo ya wuce.

GTK; Wadanne irin nasarori ne kake ganin ka cimma a wannan aiki?

NAZIFI Abdullahi; Ai narorin da na samu a wannan aiki suna nan da
dama. Don nasarori kamar na vangaren jama’a na sami nasara ta dalilin
wannan aiki, domin  shi yasa ake yi mani lakabi da muryar Unity. Kamar
yadda na fada maka, kafin na fara wannan aiki babu wanda ya sanni.

Amma a yanzu sakamakon wannan aiki  duk inda na shiga sai naga mutane
sun sanni. Bayan haka wata nasarar kuma ita ce wannan aiki ya koyar
dani tsoran Allah ya kuma koyar da ni girmama na gaba. Da mutumta na
baya.

Sannan kuma nasara ta vangaren dukiya ko kudi sai dai nace na gode
Allah. Don ina mai tabbatar maka kamar abin da ya shafi abinci da abin
sha, idan kaje gidana sai ka ture. Kuma duk ba da kudina nake saye ba.
Haka kawai sai mutum ya kirani saboda wannan aiki da nake yi, yace ga
kudi nan ya saka mani a asusun ajiyata na banki. Ko a ‘yan kwanakin
nan akwai wasu makudan kudi da wani mutum ya bani, da na karva sai da
na dada jinjinasu naji dadi kuma a zuciyata nace lallai wannan aiki ne
wanda mutum zai kara rike shi hanu bibbiyu.

Bayan haka na sami kyaututtukan karramawa da dama  daga kungiyoyi
daban dabam  a wannan gari na Jos.

Wasu suna cewa aikin jarida ba aiki ne da ake samun kudi ba, ko kuma
‘yan jarida suna mutuwa a talauce ba, ni ban yarda da wannan ba. Domin
kamar yadda ka ganni yanzu ta dalilin wannan aiki ina da gida da fili
nawa na kaina. Ina da duk wani abu na rayuwa ta dalilin wannan aikin
jarida. Saboda haka ni babu abin da zance a kan wannan aiki sai dai
nace na gode Allah.

GTK; Mene ne sakonka ga al’umma musamman matasa masu sha’awar wannan aiki?

NAZIFI Abdullahi; Sakona ga al’umma musamman masu sha’awar wannan aiki
na jarida shi ne duk wanda ya sami kansa a wannan aiki, ya rike hakuri
da gaskiya. Kuma ya zamanto mai jajircewa mai tausayin na baya tare da
girmama na gaba. Idan har mutum ya rike wadannan abubuwa zai sami
nasara. Don aikin jarida gaki daya aiki ne na gyara  tarbiya, idan
babu girmama mutane, ba zaka tava zuwa ko’ina ba, idan baka da godiyar
Allah ba zaka tava zuwa ko’ina ba. Don haka sakona ga matasa masu
sha’awar wannan aiki shi ne su rike gaskiya su girmama na gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.