Ana Binciken Sanadiyyar Hadarin Jirgin Rasha

0
1045

KAMFANIN jirgin saman Rasha da jirginsa ya yi hadari a yankin Sinai na kasar Masar, inda mutane 224 suka rasu, na cewa wani abu da ya faru daga wajen jirgin saman ne kadai, ake ganin zai kasance musabbabin hadarin.

Mataimakin daraktan kamfanin na Metrojet, Alexander Smirnov ya ya fdi haka ga manema labarai a Masko a inda ya kawar da yuwuwar tangardar na’urar, yana mai cewa wani abu ne daga wajen jirgin saman za a iya dangantawa
da hadarin na ranar Asabar.

Mai magana da yawun shugaba Putin, Dmitry Peskov ya ce shugaba Putin zai gana da ministan sufurin kasar wanda ya je wajen da jirgin ya fadi domin yi masa bayani.

Mr Peskov ya fada wa kafar yada labarai ta BBC cewa ana ci gaba da bincike a kan musabbabin faduwar jirgin, amma ya yi gargadi kan yada jita-jita kan cewa ‘yan ta’adda ne suka harbo jirgin.

Yanzu haka an kai gawarwakin mutane sama da dari da arba’in zuwa birnin St Petersburg.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.