Da Gwamnati Ta Rage Kudin Mai Za Mu Rage Kudin Shiga Mota—Isah Ibrahim

0
695

Isah Ahmed, Daga Jos

MATAIMAKIN shugaban kungiyar direbobi ta kasa [NURTW] na tashar mota ta Student Village da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato, Malam Isah Ibrahim ya bada tabbacin  cewa idan har gwamnatin Nijeriya ta
rage kudin mai,  to babu shakka kungiyarsu za ta rage kudin shiga mota 
da suke karba a wajen fasinjoji.

Malam Isah Ibrahim ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.


Ya ce idan aka rage kudin mai a kasar nan za mu rage kudin shiga mota, 
kuma za mu rage yawan mutanen da ake cusawa a mota, musamman a gaban mota  daga mutane biyu zuwa mutum daya.


Ya ce rage kudin man fetur zai yi matukar taimaka wa al’ummar kasar nan 
domin  shi ne kashin bayan komai na harkokin rayuwa a Nijeriya.

Don haka ya bukaci gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari ta dubi wannan al’amari na rage farashin mai a kasar nan domin al’ummar kasar nan su sami saukin rayuwa.
Har’ila yau ya yi kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari kan ya duba matsalar lalacewar hanyoyin mota a kasar nan. Ya ce  ”muna fama da matsalar lalacewar hanyoyin mota a kasar nan.

Duk hadarurrukan da suke faruwa a kasar nan, suna faruwa ne sakamakon rashin kyawon hanyoyin mota a  kasar nan.  Don haka muna rokon gwamnatin Buhari ta fara magance matsalar hanyoyin mota a kasar nan.


Malam Isah ya yi kira ga fasinjoji da suke shiga mota kan su guji 
shiga mota a wajen tasha, saboda hadarin da ke tattare da yin haka. Ya ce a tashoshi  ana rubuta sunaye da adiresoshi da nambobin wayoyin dukkan fasinjojin da suka shiga mota, don ko da wani abu ya faru an san inda za a binciki mutum.


‘’Amma  idan idan fasinja ya shiga mota a hanya ba za a iya yin irin wadannan abubuwa ba, kuma fasinja  zai iya haduwa da miyagun mutane kuma idan ya bata ba za a san inda za a nemi shi ba’’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.