An Bukaci Al’umma Da Su Taimaki Miskinai Da Marayu

0
591

Usman Nasidi Daga Kaduna


BABBAN limamin masallacin Juma’a na kwalejin gwamnati, wato government college Sheikh Sha’aibu Jibrin ya bukaci al’umma masu hali da su taimaki jama’a miskinai da marayu don samun babban rabo a gobe kiyama.


Limamin ya bayyana hakan ne a zantawarsa da wakilinmu jim kadan bayan kammala hudubar da ya gabatar a ranar juma’ar da ta gabata, inda ya furta cewa ba imanin kwarai ba ne mutum ya ci ya koshi bai ba da sadaka ko kyauta ga wani ba,don duk wanda ya bada kyauta ko sadakar naira daya ga mabukaci, Allah zai saka masa da alheri.


Sheikh Sha’aibu, ya kara da cewa mutanen da suka fi cancanta da a taimaka musu bayan marayu da miskinai su ne masu mutunci wadanda suka mallaki wani abu amma sakamakon yanayin rayuwa suka tsinci kansu a cikin wani hali.


Ya ce ” wannan kiran da hudubar take yi, ya shafi kowa da kowa kamar masu mulki da masu hali don duk wanda ya jikan wani musamman marayu, talakawa da miskinai, to shi ma Allah zai jikansa don ba zai tozarta aikin da ya yi ba.”


A cewarsa, ya kamata gwamnati ko masu mulki da hali su rika duba irin halin da na kasa da su ke ciki, kuma su taimaka musu musamman irin wannan lokacin da ake ciki, don ba mutane masu yawon bara kadai ne ke da bukatar taimako ba har da wasu al’ummar da suka tsinci kansu a wani hali.


A karshe, Sheikh Sha’aibu Jibrin ya yi kira ga shugabanni da su duba yanayin yadda al’amura ke tafiya a yanzu don su taimaka musu, kana ya bukaci talakawa da su kara hakuri don hakuri shi ne babban abinci ga mumini inji Manzo (SAW).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.