AN KARA WA ‘MTN’ WA’ADIN BIYAN TARA

0
715

RABO HALADU, Daga Kaduna


KAMFANIN wayar salula na MTN ya ce 
hukumomi a Najeriya sun tsawaita wa’adin da suka dibar masa domin ya biya tarar da aka sanya masa.
Hukumar da ke sa ido a kan kamfanonin sadarwa ce ta sanya wa MTN tarar Dala $5.2bn saboda ya ki rufe layukan mutanen da ba su yi rajista da shi ba har wa’adin yin rajistar ya wuce.
Hukumar ta bukaci MTN ya biya tarar ranar 16 ga watan Nuwamba, shekaranjiya kenan. 
Sai dai wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta ce, “Muna sanar da masu hannun jari a cikin kamfanin cewa, hukumomin Najeriya sun
amince su tsawaita wa’adin da suka sanya mana domin mu biya tara har sai mun kammala tattaunawar da muke yi da su”.
MTN ya kara da cewa za su ci gaba da tattaunawa da hukumomin Najeriya kan rashin rufe layukan da kuma yadda za a shawo kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.