Cika Alkawarin Honorabul Abdulmuminu Jibril Tutur Na Madalla Tir Ne?

0
1443
WANI Fasihi a fagen wake a nan kasar Hausa a cikin daya daga cikin wakokinsa ina tunawa yana cewa, ‘’In za ka fadi,fadi gaskiya komai ta ka ja maka ka biya…’’Ya ci gaba da cewa, ‘’Haka ne Editanmu na Gaskiya Wadda Ta Fi Dubun Zinariya’’.
‘Shafinmu na ’A Ganina’, a wannan fitowa a wannan jarida GTK na kasa kunnuwana ne Kano a kuma wasu mazabu biyu na dan majalisar wakilan tarayyar Najeriya mai wakiltar mazabar karamar hukumar Kiru da karamar hukumar Bebeji masu kananan mazabu har guda 29 cur, wato Honorabul Abdulmuminu Jibril.
Kyawon alkawari dai cikawa,inji masu iya magana, to, shi wannan dan majalisa a nawa binciken duk da yake ban kammala bincikena a mazabun nan 29 baki daya ba, amma na shiga wurare da dama inda na gano cewa,Honorabul Abdulmuminu Jibril sai sam-barka ake yi masa na lashe zabensa karo na biyu a tutar Jam’iyyar ta yanzu, wato APC canji. Honorabul din ga idon wasu ‘yan tsirarun mutane ya yi komai tun da suna dan samun ‘ya’yan banki a hannunsa, musamman ma idan suna da tsaurin ido na fito-na-fito da shi da sauran makamancin hakan.
To, sai dai ba a nan ‘Gizo yake sakarsa ba’, muddin aka zurfafa bincike kan wani ko kan wani abu, to, lallai ba za a sha ba. Abin da nake son in fada a nan shi ne, shi dai wannan yanki na dan majalisa wanda shi Honorabul Abdulmuminu Jibril ke wakilta a ‘yan shekarun baya an sha gwagwarmaya wajen tsayar da shi takara bayan alkawura da aka yi ta daukar wa jama’a,to,ya zuwa yanzu dai ya ci zabensa har yana cikin shekara ta biyar,amma abin bakin ciki idan na ce bai cika ko daya ba, ai ban yi zuki-ta-malli  ba, muddin ina da hujjojina a hannu.
Idan na ce hujjoji ina nufin hujjoji tsantsabaro, wato hujjoji a fili. Abin da kawai zan yi yanzu zan yi kokari in fara zayyana kadan daga cikin binciken da na yi a wannan batu. Na farko dai a zagayen da na yi na gano cewa, Honorabul din tun a wancan lokacin ya dauki alkawarin zai gyara wa jama’arsa na Gwarmai da Bebeji hanyarsu,wato hanyar Gwarmai zuwa Bebeji,sai dai al’amarin shiru kake ji kamar ‘,Malam ya ci shirwa’.
Na biyu kuma shi ne,ya yi alkawarin cewa,zai sanya aiki na Miliyan dari biyu (N200m) a Kiru da Bebeji, inda ya rantse da Alkur’ani a gaban mutane cewa, zai dawo da aikin ba da dadewa ba, domin a lokacin ya sanar da cewa, PA dinsa ya yi awon gaba da aikin, to, har yau din nan baya ga rantsuwarsa, shiru kake ji kamar an shuka dusa.
Hausawa suna cewa, ilimi gishirin zaman duniya, da gogan nawa yake daukar alkawari kan ilimi, Honorabul Abdulmuminu ya ce zai dauki nauyin karatun yara har sama da dari, amma har tsawon shekaru biyar batun daukar nauyin karatun na yara ya yi batar kwabo.
Na hudu kuma shi ne, ya yi wa ‘yan Kofa alkawarin zai gyara masu Injimin ruwa. Na biyar ma ya dauki alkawarin gyara wa ‘yan Kofa masallacin kasuwa, al’amarin da har yanzu komai ba a yi ba, wato, dai ‘’an fada ne ba a cika ba’’.
Na biyar shi ne ni ina da budaddun kunnuwa, ina zagayena ko ina a fadin Najeriya inda hali ya kai ni, kuma ina bibiyar ayyukan da ‘yan majalisa ko gwamnoni suke yi ko shugabannin kananan hukumomi.
‘Yan majalisa da dama suna kawo ayyukan gwamnatin tarayya a mazabunsu, to, wane aiki ne guda daya wanda Honorabul Abdulmuminu ya kawo a nasa yankin? Ban gan shi ba sam, kuma ni ba makaho ba ne. Kodayake na ga gidan da ya gina a Kofa,to, ko shi ne aikin na gwamnatin tarayya? Oho!
Haka kuma na ji Honorabul ya ce, ya bada sako na makudan kudade domin a tafi kasar Amurka a sayo wa kowace mazaba motar kiwon lafiya ta ta-fi-daa-gidanka, wato motocin da za su rika dawainiya tare da daukar marasa lafiya zuwa asibiti idan rashin lafiyar ta faskara.
 Kash! Allah Yana sane da cewa, zan yi kokarin in dinga rubuto hujjojina kadan-kadan a wannan jarida, kuma sam wallahi ni ban taba ko a cikin raina ba inji ina kiyayya da Honorabul Abdulmuminu Jibril ko a ce ba na sonsa ballantana a ce fada muke yi da shi, ko ina neman tozarta shi , a’a, adalcina bai wuce, idan mutum irinsa ya yi alkawari in yi kokarin in gano ko ya cika shi ne dalilin da ya sanya ake kirana ‘’Kunnen Gari’’.
Kuma wannan jarida sunanta ‘’ Gaskiya Ta Fi Kwabo’’, sannan ga mu duka muna kwaikwayon shugaban kasa ne Muhammadu Buhari.
Sai mun hadu a bugu na gaba da wasu hujjojin nawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.