Gwamnonin Najeriya Sun nuna Gazawa

0
1409

RABO HALADU,  KADUNA

Gwamanonin jihohi 36 na Najeriya sun ce
ba za su iya ci gaba da biyan mafi kankantar
albashi na Nairia 18,000 ga ma’aikatansu
ba, saboda yanayin tabarbarewar tattalin
arziki da kasar ta sami kanta a ciki.
Gwamnonin sun bayyana hakan ne a  karshen wani taron da suka yi a ranar
Alhamis a Abuja a karkashin inuwar kungiyar
gwamnoni ta Najeriya, gwamnonin sun ce
faduwar darajar mai ya yi mummunan tasiri a kan
abin da suke samu na kudin shiga.
Gwamnonin sun ce dawainiyar biyan mafi
karancin albashin ba ta da yawa a lokacin da
ake sayar da gangar mai kan dala 126, sabanin
yanzu da ake sayar da ita kan dala 41.
sun kuma bukaci su gana da Shugaba
Muhammadu Buhari, don tattaunawa kan
tattalin arzikin kasar.
Sannan sun yanke shawara cewa hanyar da
kawai za a bi don magance wannan hali na ka-
ka-ni-ka-yi shi ne a mayar da hankali kan
harkar noma da hakar ma’adinai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.