‘Yan kasuwar Jos sun bukaci shugaban kwastan ya yi bincike

0
1392

Isah Ahmed Daga Jos

‘Yan kasuwar da suke kasuwanci a kasuwar ‘yan kwalli da ke garin Jos
babban birnin jihar Filato, sun bukaci Shugaban hukumar kwastan ta
kasa Kanar Hameed  Ali mai ritaya kan ya yi binciken yadda  shinkafa da man
gyadarsu da aka kama mota uku a kan hanyar Saminaka zuwa Jos, a
kwanakin baya.

Da yake zantawa da wakilinmu kan wannan al’amari, mataimakin shugaban
kungiyar ‘yan kasuwa ta karamar hukumar Jos ta arewa Alhaji Habibu
Lawal Nalele ya bayyana cewa Jami’an kwastan sun kamawa ‘yan kasuwarmu
buhunan shinkafa da man gyada mota uku. Bayan da suka sayo a  Kano
suna dawowa a kan hanyar Saminaka zuwa garin Jos.

Ya ce wannan kamu da jami’an kwastan suka yi wa kayayyakin ‘yan
kasuwar namu, wani babban abin takaici ne, domin  wadannan kayayyaki
‘yan kasuwar namu sun sayo su ne a kasuwa.

”Mu ‘yan kasuwa mun bada gagarumar gudunmawa wajen zaben wannan
gwamnati ta yanzu, don ganin an sami canji a kasar nan. Amma sai gashi
abin mamaki jami’an kwastan suna bin mutanenmu suna kwace masu
kayayyakin da suka sayo, a cikin  Nijeriya”.

Ya ce da wuya aga dan kasuwa yaje ya sayo shinkafa a waje,  kamfanoni
ne suke zuwa su yo odar shinkafa daga waje.

Ya ce muna tunanin wasu bata garin jami’an kwastan ne suke irin wannan
aiki, na kame kamen kayayyakin ‘yan kasuwa  don bata sunan hukumar.
Don haka muna kira ga  shugaban hukumar  kwastan na  kasa Kanar Hameed
Ali  mai ritaya kan ya binciki wannan al’amari domin sanin  abin da ya
faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.