Gwamna El-Rufa’i Ya Bayar Da Motocin Tsaro 107 Ga ma’aikata

0
1375

Imrana Abdullahi Daga Kaduna

GWAMNATIN Jahar Kaduna karkashin jagorancin malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i, ta bayar da tallafin motocin gudanar da ayyukan tsaro guda 107 ga hukumomin tsaron da ke aiki a fadin jahar baki daya.

Shugaban rundunar yan sanda ta kasa da kansa yazo garin kaduna domin karbar wadannan motoci tare da rigunan sulke 230 da kananan hukumomin jahar Kaduna 23 suka sayawa jami’an tsaro a matsayin tallafi ta yadda za su samu sukunin gudanar da aiki.

Malan Nasiru El-Rufa’i,ya bayyana cewa lamarin harkar tsaro na daya daga cikin al’amuran da suka ba muhimmanci saboda komai na rayuwar duniya na samuwa ne idan aka samu ingantaccen tsaron da jama’a za su yi walwala.

“Gwamnatinmu tana gudanar da ayyuka tare da dukkan jami’an tsaron da ke cikin jahar kaduna baki daya wanda hakan ne ma yasa aka samu kwarin gwiwar gudanar da aaiki tsakanin jahohin Katsina,kaduna,Kano,Zamfara da neja da niyyar kakkabe matsalolin tsaro a wadannan jahohin ta yadda jama’a za su samu walwala”.

Ya ci gaba da cewa muna da jami’an yan sanda dubu 13 da suke aiki a fadin jahar kaduna kuma muna bukatar kari musamman ganin cewa jahar kaduna tana da kashi 5 daga cikin dari na yawan jama’ar da suke Najeriya don haka ana bukatar kashi 5 na yawan jami’an yan sandan da za  a dauka a fadin kasa a nan gaba kadan,saboda jahar kaduna na bukatar karin yan sanda dubu 7000.

Ya kuma yi godiya ga shugaban yan sanda na najeriya Mista Solomon Arase da ya turo masu kwararren dan sanda a matsayin shugaban yan sandan jahar.

Da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban yan sandan tarayyar Najeriya mista Solomon Arase, bayyana wa daukacin jama’a ya yi cewa da yardar allah ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da aikisu kuma za su yi dukkan mai yuwuwa domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Da wakilinmu yaji ta bakin jama’ar da aka yi wannan aiki dominsu sun bayyana cikakkiyar gamsuwarsu bisa wannan kokari na gwamnan jahar Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.