Za a fara kama masu Gidajen Man Da ke boye fetur

0
722

Usman Nasidi Daga Kaduna

Babban kamfanin man fetur ta kas ar Najeriya, NNPC ta nemi hukumar
tsaro ta farin kaya, DSS da takwararta da ke yaki da masu yi wa
tattali arzikin kasa ta’annati, EFCC dasu kama masu gidajen man da ke
boye fetur.

Kamfanin man ta NNPC ta ce ta nemi agajin hukumomin biyu ne a yunkurin
da take yi na magance matsalar man fetur da ake fama da
ita a sassa daban-daban na kasar.

A wata sanarwa da kakakin kamfanin, Ohi Alegbe ya fitar, NNPC ya nemi
afuwar ‘yan Najeriya saboda wahalar da suke sha kafin samun man fetur
din, kuma yana mai cewa yana daukar
kwararan matakai domin shawo kan matsalar.

Sanarwar ta kara da cewa, Sun nemi agajin EFCC da DSS ne domin su
taimaka musu wajen sanya idanu sosai akan gidajen man da ke boye shi,
kuma za su kama duk wanda aka samu yana boye man.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.