Ban Aiki Kowa Ya Tayar Da Fitina Ba – David Mark

0
746

Rabo Haladu Daga Kaduna

Tsohon shugaban majalisar dattijai
David Mark ya bukaci jama’ar
mazabarsa da kada su tayar da fitina
sakamakon soke zabensa da wata kotu ta yi.
A cikin wata sanarwa, Sanata Mark ya bukaci
jama’ar mazabar sa da kada su karaya, a
maimakon haka, su kara shiri na tunkarar
zaben da za a sake gudanarwa.
Ya ce yana da yakinin zai sake lashe zaben idan
aka sake gudanar da shi.
Wata kotun daukaka kara ce da ke zama a
Makurdi babban birnin jihar Benue ta soke
zaben da aka yiwa Sanata David Mark.
Kotun ta ce akwai kuskure a matsayin da
hukumar zabe ta kasar INEC ta dauka na
baiyana David Mark, dan takarar Jam’iyyar PDP
a matsayin wanda ya lashe zaben yan majalisar
dattijai a shiyyar kudancin Benue wanda aka
gudanar a ranar 28 ga watan Maris
Dan takarar sanata a karkashin jam’iyyar APC
shiyyar kudancin Benue Donald Onjeh shi ne ya
shigar da karar.
Kotun ta bayar da umarnin a sake zaben
kujerar majalisar dattijan cikin kwanaki casa’in.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.