Gwamnatin za ta farfado da sufurin jiragen sama a Nijeriya

0
1143

Isah Ahmed Daga Jos

Ministan kasa a ma’aikatar harkokin sufurin jiragen sama ta tarayya,
Sanata Hadi Sirika ya bayyana cewa gwamnatin tarayya zata farfado da
harkokin  sufurin jiragen sama a Nijeriya.

Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron harkokin sufurin jiragen sama
na  duniya, da aka  gudanar a birnin Montreal, na kasar Kanada.
Ya ce wannan gwamnati ta Nijeriya,  karkashin shugaban kasa Muhammad
Buhari ta kuduri aniyar sake farfaxo da harkokin sufurin jiragen sama
a Nijeriya, ta hanyar gyara tashoshin jiragen saman kasar da tare da
samar kayayyakin aiki irin na zamani  a tashoshin.

Ya ce gwamnatin Nijeriya zata yi hakan ne don ganin ta tafi tare da manyan kasashen
duniya, da suka cigaba kan harkokin sufurin jiragen sama.

A nasu jawaban daban daban a wajen taron  ministan sufuri na kasar
Kanada Marc Garneau da ministan sufuri na kasar Kolombiya da sakatare
janar na kungiyar yawon bude ido  ta duniya [UNWTO] sun bukaci
kasashen duniya su hada kai, don ganin an aiwatar da tsare tsare
bunkasa harkokin sufurin jiragen sama a duniya, don amfanin al’ummar
duniya.

Shi dai wannan taro ministan kasa a ma’aikatar sufurin jiragen sama ta
tarayya Sanata Hadi Sirika ne ya jagoranci tawagar Nijeriya, wadda ta
kun shi jakadan Nijeriya na riko a kasar Kanada  Jafar Mohammed  da
daraktocin ma’aikatar harkokin sufurin jiragen sama ta Nijeriya kuma taron  ya sami halartar wakilai daga  kasashen duniya 99.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.