Tashin Bam A Kano ya kashe mutane 21 a taron Mabiya Shi’a

0
781

Usman Nasidi
AN samu tashin bam a wani kauyen Dakasoye ta jihar Kano inda  ya kashe
akalla mutane 21 mabiya shi’a da ke tattaki daga garin Kano zuwa
Zaria.
Wani daga cikin mabiya shi’ar ya shaidawa manema labarai cewa mutane
ashirin da daya sun mutu, kuma ya kara da cewa mutane da dama sun
jikkata.
Acewarsa, daruruwan mabiya Shi’a daga arewa maso gabas da yammacin
kasar ne suka taru a Kano, inda daga nan suka nufi Zaria domin juyayin
“Yaumul arba’un”, wato kwanaki arba’in da kashe Hussain jikan manzon
Allah (SAW).
Ya kara da cewa, an fara kama wani mutum da bam din da bai tashi ba,
kuma ya ce su biyu ne ke dauke da bam din, jim kadan sai na biyun da
ke dauke da bam din ya ruga da gudu ya shiga cikin masu jerin gwanon,
inda ya tashi bam din da ke jikinsa.
A cewar sa, sun dauki gawarwakin, sannan suka ci gaba da yin jerin
gwanon zuwa Zaria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.