Rusau:Mazauna Garin Zariya Sun koka

0
1363

A kokarin da wadansu jama’a mazauna cikin birnin Zariya musamman wadanda suke zaune a bayan dakin karatu na birnin zariya da suka koka cewa wai an ba su wa’adin su kwashe ina su ina su su bar wannan wuri hakan yasa suka taso kwansu da kwarkwatarsu zuwa cibiyar manema labarai ta jahar kaduna domin bayyana korafinsu.

Su dai wadannan mutanen sun iso cibiyar manema labarai ne a cikin motocin haya na Bas bas  da kuma kananan motocin daga birnin zariya domin kawai su bayyana rashin jin dadin su da kuma fargabar da suke da ita na wa’adin kwanaki 21 da suka koka kan cewa gwamnatin jahar kaduna ta ba su na su kwashe daukacin abin da suka mallaka domin za a rushe gidajen nasu.

Tawagar da ta kunshi mata da maza manya da kananan yara sun bayyana cewa lallai suna da fargaba a game da wannan matsalar rusau da za su fuskanta a nan da yan kwanaki kamar yadda gwamnatin jahar ta ba su wa’adi.

 

 

 

 

amma kamar yadda bayanai suka fito daga wajen gwamnatin jahar kaduna na bayanin cewa ba wai suna fada da wani ko wasu bane illa dai kawai ana yin aiki ne tare da bin ka’ida saboda haka duk wanda yake da takardun da suka bayyana cewa filin nasa ne to ya kawo takardun a duba domin tabbatar da cewa nasa ne ya mallaka domin biyan diyya kamar yadda aka shardanta.

Idan dai za a iya tunawa gwamnatin jahar Kaduna karkashin jagorancin malam nasiru Ahmad El-Rufa’i ta sha bayyana cewa tana aiwatar da aikin dawowa da gwamnati filayenta ne da aka mamaye tun can baya.

Kamar yadda suka bayyana wa manema labarai cewa “mu dai talakawa ne kuma bamu mallaki komai ba sai wadannan gidaje don haka muna son ayi mana adalci a kuma tausaya mana”inji su.

Sun shaidawa manema labarai cewa hakika mu da muke zaune a wadannann wuraren da aka ba su wa’adin kwanaki 21 da cewa za’a yi mana rusau din gidajenmu bama jin dadin wannan lamari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.