Yunkurin farfado da PDP ihu bayan hari ne–Yahaya Kega

0
609

Isah Ahmed, Jos

Alhaji Yahaya Muhammad Kega, fitattacen dan siyasa ne a jihar Filato kuma shi ne  shugaban kungiyar dillalan motoci ta Nijeriya reshen jihar Filato. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana cewa yunkurin da wasu shugabannin jam’iyyar PDP suke yi na sake farfado da jam’iyyar don tunkarar zaven shekara ta 2019 ihu bayan hari ne kuma yaudara ce.

Har’ila yau ya yi bayanin tsare tsaren gina kasar nan da gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari ta kawo.
Ga dai yadda tatattaunawar ta kasance

GTK; A yan kwanakin nan jam’iyyar adawa ta PDP  tayi tarurruka don sake farfado da  jam’iyyar, don  tunkarar zaben shekara ta 2019, shin  kana ganin za su cimma nasara kuwa?

Yahaya Kega; Ai, wannan yunkuri da jam’iyyar PDP suke yi na sake farfadowa magana  ce kawai , kuma ihu bayan hari ne. Abin da ya kamata su yi a cikin shekaru 16, ko kwata  ba su yi ba.

Yanzu daga hawan wannan sabuwar gwamnati watanni biyar da suka gabata ke nan, har an ga banbancin da ba a taba gani ba a cikin shekaru 16 da jam’iyyar PDP tayi tana mulkin kasar nan.  Kuma wannan sabuwar gwamnati mai mutumci ce. Domin ita gwamnati, sai ta kama mutumcinta kafin jama’a su goyi bayanta.

Kuma wadannan mutane na PDP sune dai ba wasu bane daban, kuma sune suka saba da irin wadannan miyagun abubuwa sune suka saba da  cin hanci da rashawa, sune suka saba da yin ba daidai ba. Za su canza kansu
ne ai komai canjin da zasu yi ba zai yuwu ba. Domin ba zasu canza kansu ba, su koma wasu mutane daban ba. Domin mutanen da aka sani ne mutanen da suka cuci al’ummar kasar nan ne, mutanen da suka rikirkita kasar nan ne, sune kuma za su zo su ce wai sun dawo za su yi wani gyara?

Saboda haka wannan yunkuri da  suke yi ba wani abu bane sai yaudara kawai. Shawarata a gare su ita ce su tsaya su koyi adawa daga nan har zuwa shekaru 16 masu zuwa, in suna da rabo sa kama. Amma a yanzu kan mage ya waye, talakawa sun riga sun gane an bude masu ido. Don haka an riga an wuce maganar jam’iyyar PDP a Nijeriya.

GTK;  To, maye zaka ce dangane da rantsar da ministocin da shugaban kasa Muhammad Buhari, ya yi a makon da ya gabata?

Yahaya Kega; Dama rashin hakuri ne yasa aka yi ta nuna mutsuwa kan shugaban kasa Muhammad Buhari ya nada ministocinsa. Amma da mutane sun yi tunani ai tsarin mulki ne ya nuna cewa  dole ne shugaban kasa ya sami majalisar zartarwarsa. Wadanda zasu rika shawarta abubuwan da za a yi a kasa.  Amma dole ne a bashi lokaci don ya zabi mutanen da zai yi aiki da su. Domin ba abu ne wanda za a ce a rana daya shugaban kasa ya ce ya nada wane ya nada wane ba. Dole ne sai ya ga irin mutanen da suka dace ya tafi dasu. Wannan shi ne abin da ya faru ga shugaban kasa Muhammad Buhari.

To, yanzu mun gode Allah an rantsar da wadannan ministoci kuma an raba masu ma’aikatu.  Ada shi kadai yake yin aiki, yanzu kowace ma’aikata ta sami jagora wanda zai jagoranci wannan ma’aikata. Kuma wadannan ministoci sun san irin wannan gwamnati kuma sun san abin da shugaban kasa zai iya yi, sun san abin da ba zai iya yi ba. Duk mutumin da zai yi aiki da  shugaban kasa Muhammad Buhari dole ne ya tsaya ya yi gaskiya ya yi aikin da aka bashi.

GTK; Kamar wadanne abubuwa ne kake ganin ya kamata waxannan ministoci su fi mayar da hankali a kai?

Yahaya Kega; Abin da ya kamata waxannan ministoci su mayar da hankali a kai shi ne na farko jam’iyyar APC ta ce tazo ne domin ta kawo canji. Wato ta ce tazo ne domin ta kawo gyara kan abubuwan da suka lalace a kasar nan.

Babu shakka wadannan ministoci da shugaban kasa Muhammad Buhari, ya nada, mutane ne da suka sun san abubuwan da suka lalace a kasar nan. Abubuwa ne da ada ake yin su kara zube, babu doka da oda ana debo
kudin jama’a ana kawowa ma’aikatu, maimakon ace ga ayyukan da ya kamata ayi, don cigaban kasa sai wasu ‘yan tsirarun mutane su  wawushe kudaden da aka kawo, su sanya a aljihunsu. Sai a watsar da ayyukan da aka ce ayi har ayi shekara da shekaru ba a kammala   wadannan ayyukan ba.

To, a wannan karon muna son mu ga ayyuka  a kasa komai kankantarsu. Ba wai yawan kudin da za a baiwa wadannan ministoci ba.  Domin abin da aka sani ada ana kawo kudi da yawa amma ba a ganin ayyukan da ake yi a
kasa. Saboda ada da an kawo kudi za a raba ne kawai amma a yanzu duk kudin da suka zo   komai kankantarsu za a yi ayyukan ci gaba. Banbancin wannan gwamnati da gwamnatin da ta gabata ke nan, abin da ya kamata wadannan ministoci  suyi ke nan.

GTK; Ya ya kake ganin tafiyar wannan gwamnati kan maganar yaki da cin hanci da kuma baiwa bangaren shari’a yanci?

Yahaya Kega; Ai,  yanzu ne aka san ana yin gwamnati domin an baiwa kowa hakkinsa, kowa yana aikinsa batare da katsalandan ba. Dama ai bangaren shari’a, bangare ne mai zaman kansa a tsarin mulkin kasar nan. Amma ada wannan bangare bai sami wannan dama ba. Domin gwamnati tana yiwa wannan bangare katsalandan a cikin al’amarunsu, abin da ya kamata masu shari’a suyi  mutane suna gani kiri-kiri sai a juye shi rana daya.  To, amma wannan gwamnati ba haka take ba.

Domin idan ka lura yanzu ko waye kai,  idan kayi za a yi maka, amma ada idan kai wani ne ba a isa idan kayi aje a yanke maka hukumci ba. Amma yanzu kowa ya san idan ya yi za a yi masa.

Bayan haka maganar yaki da cin hanci da rashawa, ai sai kaga shugabanka yana cin hanci da rashawar kafin kai ma ka koya.  Idan aka ce na gaba ya gyaru, kai ma idan aka ce kayi ba zaka yi ba, domin idan kayi ba zai barka ba.

Don haka dole kowa ya sani cewa wannan yaki da cin hanci da rashawa da wannan gwamnati ta fito da shi, ba da wasa take yi ba. Don haka muna yi masu fatan alheri kuma muna yi masu addu’a kan wannan kuduri nasu.

GTK; A matsayinka na shugaban kungiyar dillalan motoci ta Jihar Filato maye zaka ce dangane da tafiyar hukumar kwastan, karqashin jagorancin sabon Kantoman hukumar Kanar Hameed Ali mai ritaya?

Yahaya Kega; Kowanne yanayi da yadda yake tafiya, shi wannan sabon shugaban hukumar kwastan ta kasa Kanar Hameed Ali mai ritaya yana aiki da wannan sabuwar gwamnati wadda take da matakai daban daban na kawo canji ne. Saboda haka dole a sami canje-canje a wannan hukuma.

Abu daya ne kawai muke son shugaban hukumar nan ya rika dubawa, maganar ya zauna a ofis kawai ya ce ya kara kudin harajin shigo da kaya ba shi ne ba.

Ya duba yaga  mene ne  zai amfani talakawa da kasar nan gabaki daya.Ba wai maganar kudin shiga ba. Yanzu kaga kamar mu masu sayar da motoci an kara mana kudaden harajin shigo da motoci, wannan abu ba a kanmu
zai tsaya ba, zai tsaya ne  kan masu saye da masu shiga mota. Saboda haka idan za a yi abubuwa a wannan hukuma, a rika dubawa aga da waye da waye zai shafa. Abubuwan da ake yi wadanda basu da kyau ada a wannan hukuma, sune ya kamata a kawar a kawo abubuwa masu kyau, yadda al’ummar kasa za su amfana gabaki daya.

GTK; A karshe wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar kasar nan?

Yahaya Kega; Sako na ga  jama’ar Nijeriya  shi ne mun soma  gani a kasa a wannan sabuwar gwamnati. Mun soma ganin irin kokarin da  wannan gwamnati take yi kan harkokin tsaro da yaki da cin hanci da rashawa. Kai ma da kanka  yanzu idan aka ce kaci hanci  zaka ji tsoro, wadanda suka ci hancin ma suna dawo dasu don su huta.

Mun ga yadda ake gudanar da gwamnati ta gaskiya da yadda aka gudanar da gwamnati ta  wasa ada. Domin a gwamnatin da ta gabata wasa ne ake yi kawai. Haka kuma mun ga yadda alkalai suka canja a kasar nan, saboda sun san idan suka yi irin hukumcin da suke yi a baya suma za a hukumtasu.

Saboda haka ina kira ga jama’ar kasar nan, kan mu cigaba da yiwa wannan gwamnati addu’a tare da bata goyan baya domin ta cimma nasara kan kudurorin da ta sanya a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.