An Kwana Ana Ruwan Wuta a Zariya

0
1113

Rahotanni daga garin Zaria  da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya na cewa an kwana ana jin karar harbe-harben bindiga a unguwar Gyallesu da kewaye.
Rahotanin sun kuma ce sojoji sun yi wa gidan shugaban mabiya kungiyar ‘yan uwa musulmi ta shi’a Sheik Ibrahim Yakubu El zazaky da kuma wasu mabiya da ke Husainiyya kawanya .
Rikicin dai ya fara ne tun ranar Asabar lokacin da Babban hafsan rundunar sojin kasa ta Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai ya je wucewa ta kusa da inda mabiya Shi’ar ke taro a cibiyar Husainiyya, inda aka tsare masa hanya,
tare da kai masa hari.
Haka kuma rundunar sojin Najeriya ta zargin mabiya kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta Shi’a da kai harin, amma sun musanta.
Wannan kawanyar da aka yi wa mabiya shi’ar ta sa ‘yan uwansu da ke wasu jihohin Najeriya shiga zanga-zanga a Kano da Katsina.
Haka kuma abin bai yi wa mabiyan dadiba  ganin cewa ana takura masu a kan abin da bashi  da  tushe balentana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.