Kungiyoyin Addinai Sun Bukaci Da Ayi Bincike

0
768

Rabo Haladu Daga Kaduna
kungiyoyin addinai a tarayyar Najeriya   sun
bukaci a gudanar da bincike kan lamarin da
ya faru tsakanin ‘yan Shi’a da sojoji a
Zariya.
Kungiyar Kiristoci ta CAN ta yi kira ga
hukumomin kasar  da su bincika musabbabin
kashe-kashen da aka yi, don hana rikidewar
rikicin zuwa wani abu dabam.
CAN ta nemi a koyi darasi daga rikicin Boko
Haram.
Ita ma kungiyar Jama’atul Nasrul Islam ta
bukaci gwamnati ta kafa kwamitin bincike
domin gano abin da ya janyo mutuwar mutane
a rikici tsakanin ‘yan Shi’a da sojoji.

Majalissun dokokin kasar nan su ma sun kafa
kwamitin domin binciken lamarin.
Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi
II ya ce bai kamata kungiyoyin addini su rika
keta dokokin kasa ba, yana mai karawa da
cewa bai kuma kamata hukumomi su yi amfani
da karfin da ya wuce kima kan ‘yan kasar ba.
Tuni shugaban Iran, Hassan Rouhani ya kira
shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ta wayar
tarho domin nuna korafinsa a kan kashe ‘yan
Shi’a da sojoji suka yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.