Shan Taba Da Kwankwadar Barasa Na Haifar Da Cutar Daji

0
439

Rabo Haladu Daga Kaduna

Wani sabon binciken kimiyya da aka yi a
Amurka ya nuna cewa yawan shan taba da
kwankwadar barasa ne ke sa mutane na
kamuwa da kashi 90 cikin dari na cutar
daji, wato cancer.
Masu bincike a Jami’ar Stony Brook da ke New
York sun bayyana haka ne bayan sun sake yin
nazari kan dalilan da ke haddasa kamuwa da
cutar.
Sun gano cewa ba kasafai sauyi a fasalin jerin
kwayoyin halittar gado shi kadai  kan haifar da
cutar daji ba, ba tare da gudunmawar wani abu
daga waje ba, kamar gurbatacciyar iska da
hasken rana mai cutarwa.
Binciken, wanda aka wallafa a mujallar kimiyya
ta ‘Nature’, zai taimaka wajen sake yin nazarin
yadda za a yi rigafakin kamuwa da cutar.
Wannan binciken dai ya karyata binciken da
aka gudanar kafinsa, wanda ke ganin ana
kamuwa da cancer ne kawai sakamakon sauyi a
fasalin jerin kwayoyin halittar gado.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.