Zamba Da Rashin Aikin Yi Ne ke Kawo Rikici- Mathew Kuka

0
589

wasu masana da kuma masu son a zauna lafiya tsakanin mabiya addinin Musulunci da na Kirista a  Najiriya sun
gudanar da taro a Abuja domin lalubo hanyoyin kyautata dangantaka tsakanin mabiya addinan biyu.
Masana daga kasashe daban-daban ne suka halarci taron na hadin gwiwa   tsakanin cibiyar Kukah   da kuma cibiyar Katolika da ke kasar Amurka.
Farfesa Abdullahi Ashafa, malami a jami’ar jihar Kaduna ya ce siyasa na daya daga cikin abubuwan da ke bata zama tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya da wasu kasashen Afirka.
Ya ce saboda son zuciya, wasu mutane idan sun fadi zabe, sai su dora hakan a kan bambancin addini  da kabila, daga nan kuma sai fitina ta tashi.
Bishop Mathew Hassan Kukah, ya ce talauci da rashin wasu abubuwan more rayuwa, kamar lantarki, da rashin aikin yi, da kuma zamba, su suka fi janyo rikici da ake dangantawa da
addini. Haka kuma matsalolin  rayuwa da jama’a  suke shiga shima yataimaka gaya wajan ta da fitintinu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.