APC Tayi Allah Wadai da kalaman Sanata Shehu Sani.

0
811

Rabo Haladu Daga Kaduna
Jamiyyar APC ta jihar Kaduna ta mika goron gayyata ga dan majalisar dattawa mai wakiltar  kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Nijeriya Sanata Shehu Sani, da ya gurfana a gaban kwamitin ladaftarwar jamiyyar domin ya amsa wasu  munanan kalamai da ta ce Shehu Sani ya yi a kan Shirin Shugaban kasa   Muhammadu  Buhari na yaki da cin hanci da rashawa.
Jamiyyar APC tayi Allah wadai da irin kalaman da shi Shehu Sani, yayi da  wasu kafafan yada labarai inda  yake zargin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sanya siyasa cikin yaki da  cin hanci da rashawa.
Awani taron manema labarai da jamiyyar ta kira a jiya talata, wanda Shugaban ta  na riko wanda shima Sanata Shehu Sani yace baisan da shiba Alhaji Shuaibu Idris ya jagoranta, tace tana amsa wasu tambayoyi guda biyar domin yafitar da ita jamiyyar daga cikin duhun kalaman. Acewarta sanata Shehu Sani, ya aikata manyan zunuban da ya zama dole akan jamiyyar da ta gayyace inda ta zargi shi Sanata Shehu Sani, da  yiwa jamiyyar zagon kasa na rashin yin biyayya ga kalaman Shugaban kasa da rashin yiwa jamiyyar  biyayya da kuma  tunzura wasu matasa daga kudancin kaduna da suyiwa gwamnati bore.  Haka Kuma jamiyyar tana zargin Sanata da kokarin tada zaune tsaye na tunzura wata  kungiya domin yjwa gwamnati tawaye.
Alhaji Shuaibu Idris, yace Sanata Shehu Sani, yayi wasu kalaman da suka saba da manufofin jamjyyar wanda  a cewarta, yayi sune ba da yawunsuba. Acewar  jamiyyar ta baiwa Sanata Shehu Sani wa adin kwana bakwai da ya gurfana a gaban kwamitin idan bai yi hakan ba zai fuskanci hukuncin da yayi dai  dai da laifin  da ya aikata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.