Za A Binciki Kamfanin Jiragen Sama Na Aero

0
598

Isah Ahmed Daga Jos

Ministan ma’aikatar harkokin jiragen sama ta Nijeriya Sanata Hadi Sirika, ya bada umarnin a binciki kamfanin jiragen saman   mai suna Aero Contractors.  Za a gudanar da binciken ne saboda amfanin da tsani wajen sauko da fasanjojin da suka shigo Jirgin, a karshen makon da ya gabata a filin saukar jiragen sama na garin Bauchi.

Ministan ya ce ya sami rahotan cewa wannan kamfani ya yi amfani da tsayi wajen sauke fasinjojin da ya dauko, a filin saukar jiragen sama na garin Bauchi, a ranar asabar din da ta gabata. Ya ce wannan abu da wannan kamfani ya yi sabawa ka’idojin aikin sufurin jiragen sama na Nijeriya, da na duniya gabaki daya.

Ministan ya ce wannan bincike da za a yiwa wannan kamfani, ana son a gano dalilan da suka sanya, ya yi amfani da tsanin wajen sauko da fasinjojin da ya dauko, wanda yake da matukar hadari don ganin irin haka bata sake faruwa ba, a filayen saukar jiragen sama na kasar nan.

”Hakkin Ma’aikatar sufurin jiragen sama ta Nijeriya ne, taga cewa ta tsaya wajen ganin an yi amfani da kayayyakin aikin da ba zasu kawo hadari ga fasinjojin da suke shiga jirage a filayen jiragen sama na kasar nan ba. Don haka wannan aika-aika da wannan kamfani ya yi, bada sanin hukumar jiragen sama ta Nijeriya [FAAN] ya yi ba”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.