Dasuki na fuskantar sabuwar tuhuma a Kotu

0
510

Daga Usman Nasidi

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon mai
bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Sambo Dasuki da wasu mutane uku a gaban kotu a Abuja, a kan wasu sababbin
tuhume-tuhume 19 da suka shafi zamba.

An gurfanar da Dasuki ne tare da Shuaibu Salisu,
da Aminu Baba-Kusa da kuma wasu kamfanoni bisa zargin sace kudaden al’umma.

Ana zargin su ne da karkatar da fiye da naira
biliyan 13 daga asusun gwamnati, amma dukkansu su musanta wannan zargin.

Mai shari’a Hussein Baba Yusuf ya dage sauraron karar zuwa ranar Talata domin duba batun beli.

EFCC na zargin wadandan mutanen ne da rarrabar
da kudaden gwamnati ga ‘yan jam’iyyar PDP a lokacin zaben fitar da gwani a lokacin tsohon
shugaban kasa Goodluck Jonathan yana neman
PDP ta tsayar da shi takara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.