Jahar Kogi ta kara kafa wani tarihi

0
1185

Rabo Haladu Da Imrana Abdullahi Daga Kaduna
An rantsar da Yahaya Bello a
matsayin sabon gwamnan jihar Kogi, ba
tare da mataimakinsa James Faleke ba.
Babban jojin jihar Nasir Ajana ne ya rantsar da
sabon gwamnan a ranar Laraba.
Sai dai Shugaban kwamitin yada labarai na
kwamitin da jam’iyyar APC ta kafa na shirya
rantarwar Isiaq Ajibola, ya tabbatar wa da manema labarai
cewa Faleke bai halarci wajen rantsarwar ba.
Faleke ya kauracewa rantsarwar ne saboda
matakin da jam’iyyarsa ta dauka na kin neman
kotun sauraron kararrakin zabe ta tabbatar da
shi a matsayin sabon gwamna, bayan mutuwar
yarima Abubakar Audu.
Wannan ne dai karo na farko da aka taba
rantsar da gwamna ba tare da mataimaki ba a
tarihin siyasar Najeriyar.
Sakamakon faruwar irin wannan al’amari na rantsar da gwamna ba tare da mataimakin da za a CE an Zane su tare ba yasa ma su fashion bakin al’amura ke cewa hakika jahar Kogi ta kara ajiye wani tarihin da za a CE ba kasafai ake samu ba musamman idan akayi LA akari da iron yadda al’amura me faruwa a jahar.
Misali Lamar a kwanan baya jahar ta ysinki kanta a cikin wani tarihin da ba a taba samu ba kuma lamarin da ko a cikin kundin tsrin mulkin Najeriya ba shi da hukuncin da za a iya bugun kirji ace za a warware shi,inda ana tsaka da zaben gwamna a jahar ta Kogi sai dan takarar da shi ne a gaba wajen yawan kuri’a a rasu wanda hakika ya jefa Najeriya cikin wani hali.
Kuma tun da hakan ta faru ake ta samun rikici musamman a kan wannan kujera inda fan takarar PDP wanda shi ne gwamnan jahar a wancan lokaci yake ikirarin shi ya lashe zabe kuma wanda ya tsayawa dan takarar gwamnan da ya mutu yake cewa shi ne APC za ta tsayar takara domin ya gaji wanda suka tsaya tare har ta kawo yau ranar 27 ga watan daya na shekarar 2016 aka rantsar da gwamnan da ya gaji na PDP a jahar Kogi da ke arewacin tarayyar Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.