An tsinci gawar matashi rataye a Katsina

0
601

Daga Usman Nasidi

A ranar Juma’ar da ta gabata ne da misalin karfe 3:00 al’ummar Unguwar Sabon Gida da ke garin Katsina suka tashi da wani abin tashin hankali na ganin gawar wani saurayi mai kimanin shekara 17 a rataye da igiyar da aka sarkafo a reshen wata itaciyar kuka.

Kamar yadda ganau da suka nemi a sakaya sunayensu suka ce, an ga gawar matashin ne da mutuwarsa ta ba kowa mamaki, inda ake zargin matashi ne ya rataye kansa.

Majiyar yace “Na taba ganin gawar wani Ibo a Kudu wanda ya rataye kansa har ya mutu amma ba kamar yadda na ga gawar wannan yaron ba.

Na farko dai igiyar da aka sanya da yadda aka daura a itaciyar da irin yadda gawar take a durkushe in da shi ne ya rataye kansa jin zafin makara zai sa ya mike tsaye ya kwance igiyar daga wuyarsa ba tare da wata wahala ba,” inji daya daga cikinsu.

Daya shaidar ya ce, “babu wata alama da ta nuna cewa ga wani abin da ya taka ya hau har ya rataye kansa ya mutu, Kuma babu wasu alamu na cewa ko ya yi ’yan fizge-fizge da kafafunsa a lokacin fitar rai, ko samun alamun fitsari ko bayan gida wadanda dukkansu alamu ne da ke samuwa ga wanda ya mutu ta hanyar rataya.

Kuma wani aba inin da ya kara daure wa kowa kai shi ne, marigayin yaro ne karami wanda bai wuce shekara 17 zuwa 18 ba, kuma yanayin almajirai gare shi, sannan babu wata alama da muka gani ta an fasa jikinsa ko an yanki wani abu.

Kawai dai yara sun zo sun ce ga wani can tun dazu yake durkushe da igiya a wuyansa amma ba ya motsi, sai da muka je muka ga wannan abin mamaki.”

Jama’ar yankin na zargin cewa, akwai yiwuwar bayan an tafi Sallar Juma’a ne kafin a dawo abin da ya faru ya faru. Kuma wasu mutanen yankin sun yi zargin cewa an kashe shi ne a wani wuri aka zo nan aka rataye shi don a nuna shi ya kashe kansa Duk kokarin da

A Binciken da aka yi don gano ko akwai wanda ya san saurayin a yankin ya ci tura, inda mutanen yankin suka ce babu wanda ya san shi balle sanin sunansa ko daga inda ya fito kamin ’Yan sanda sun dauke gawarsa zuwa babban asibitin Katsina.

Mai Unguwar Sabon Gida Alhaji Kabir Sani ya ce, an zo an shaida masa ganin gawar inda ya yi hanzarin shaida wa Magaji Madu da ke gaba da shi, suka je suka ga gawar suka kuma shaida wa ’yan sanda.

Mai unguwar ya ce, saurayin ba dan unguwar ba ne, kuma ba su san daga ina ya fito ba balle wani bayani a kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.