An rantsar da Ali Modu Sheriff Sabon Shugaban Jam’ iyar PDP na kasa.

0
708

 

Rabo  Haladu Daga Kaduna

AN rantsar da tsohon gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff, a matsayin sabon shugaban  jam’iyyar adawa ta PDP a jiya ranar Litinin.
Sheriff, wanda ya koma jam’iyyar daga jam’iyyar APC ya karbi ragamar shugabancinta ne daga Prince Uche Secondus, a wajen wani takaitaccen biki da aka gudanar a hedikwatar jam’iyyar da ke
Abuja.
SAS, kamar yadda ake yi masa lakabi, ya karbi shugabancin jam’iyyar ne bayan da majalisar zartarwar jam’iyyar ta zabe shi a zaman shugabanta a ranar Talatar makon da ya gabata.
Sai dai wasu manyan shugabannin jam’iyyar sun nuna matukar adawa da zaben nasa.
A ranar Lahadi ma wata kungiyar wasu kusoshin jam’iyyar da ake kira PDP Rescue Group, ta yi kira ga Ali Sharif da ya yi murabus.
A cikin jawabinsa ya yi alkawarin sake mayar da jam’iyyar kan turba da kuma mayar da ita jam’iyyar da talakawa za su dinga jujjuya al’amurranta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.