Wahalar Mai Na Karuwa A Najeriya

0
382

Rabo Haladu Daga Kalina

Matsalar karancin man fetur ta kara ta’azzara, abin da ke jefa masu
abubuwan hawa cikin mawuyacin hali.
A wasu wuraren ciki har da Kaduna, Kano, Abuja, mutane kan shafe kwanaki biyu a
kan layi a gidajen mai kafin su kai ga samun
man, a yayin da wasu kuma suka gwammaci
saye a wurin ‘yan bumburutu.
Bayanai sun ce haka lamarin yake a sassa
daban-daban na Nijeriya musamman ma a cikin
manyan biranen inda akwai dimbin ababen
hawa.
Sai dai kamfanin man fetur NNPC, ya
ce matsalar ta samo asali ne sakamakon gibin
da aka samu wajen samar da man a sanadiyar
fasa bututan mai, da kuma jinkirin shigowa da
tataccen man daga kasar waje.
Kakakin kamfanin na NNPC, Mista Ohi Alegbe,
ya kara da cewa nan ba dadewa ba, za a
magance matsalar, kana man zai wadata a
gidajen mai.
A duk fadin kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.