An Samu Gawar Hafsan Sojan Da Aka Sace A Kaduna

0
742

IMRANA ABDULLAHI Daga Kaduna

RUNDUNAR sojan Najeriya ta bayyana cewa ta samu gawar babban Hafsan sojan da wasu masu satar mutane suka sace a garin Kaduna.

Wannan sanarwar ta fito ne daga wajen mai rikon kujerar babban Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojan Najeriya Kanar Sani Usman Kuka Sheka

Rundunar sojan ta bayyana cewa ta samu gawar Kanar Sama’ila Inusa a kauyen Ajyaita da ke wajen babban titin gwamnatin tarayyar ta Gabas.

Kanar Sama’ila Inusa dai an sace shi ne a ranar Lahadin da ta gabata an kuma samu gawarsa da misalin karfe 6:00 na yamma. Binciken da rundunar sojan ta ce ta gudanar ya nuna cewa mai yuwuwa hafsan sojan an kashe shi ne a ranar da aka sace shi saboda an samu gawarsa har ta fara tabuwa a inda aka same ta a kauyen Ajyaita da ke wajen babban titin gwamnatin tarayya na Gabas da ke Kaduna.

Rundunar sojan ta kuma lashi takobin cewa za ta tabbatar da zakulo wadanda suka yi wannan aika-aikar domin fuskantar hukunci kamar yadda doka ta tanadar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.